Kamfanin Sin Ya Kammala Aikin Layin Dogo Mai Nauyi A Kan Hamada Irinsa Na Farko A Afirka
[ad_1]
An kammala aikin shimfida layin dogo na Western Mining na kasar Algeria, wanda ya kasance layin dogo mai nauyi da aka shimfida a kan hamada irinsa na farko a Afirka, a ranar Talatar da ta gabata, kamar yadda kamfanin da ya yi aikin na kasar Sin ya sanar a jiya Laraba.
Layin dogon mai tsawon kilomita 575 shi ne mafi girma guda daya a bangaren ayyukan samar da ababen more rayuwa da wani kamfanin kasar Sin ya gudanar a kasar Algeria. Kamfanin gine-ginen layukan dogo na kasar Sin (CRCC) da kamfanonin gwamnatin kasar ta Algeria ne suka gudanar da aikin tare.
Tawagar masu gine-gine daga kasashen biyu sun yi aiki na fiye da watanni 24 a karkashin yanayi mai kalubale na hamadar Sahara. Ta hanyar ingantaccen tsari da kyakkyawar kulawar kasashen biyu, an kammala shimfida layin dogon watanni uku kafin lokacin da aka tsara. An samar da jimillar na’urorin hada dakalin siminti na layin dogo miliyan 1.1, kana aka shimfida layin dogon mai tsawon fiye da kilomita 580 tare da yi masa walda.
Layin dogon na Western Mining wani muhimmin aiki ne na shawarar Ziri Daya da Hanya Daya (BRI) da aka tsara don sada yankin ma’adanai da yankunan masana’antu da kuma tashoshin jiragen ruwa da ke kudu maso yammacin Algeria. Ana sa ran bayan kammala shi zai karfafa hanyoyin sufuri da kuma tallafa wa ci gaban tattalin arzikin yankin. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link