Mutum biyar sun mutu a hatsarin mota a Jigawa
[ad_1]
Wani hatsarin mota da aka yi a ranar Laraba a Jihar Jigawa ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane biyar yayin da wasu kuma suka jikkata.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa, SP Shiisu Lawan Adam ne, ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikawa manema labarai a Dutse babban birnin Jihar a Jigawa.
SP Shiisu ya ƙara da cewa, lamarin ya faru ne a ƙauyen Bandawa na ƙaramar hukumar Ringim, a sakamakon ƙoƙarin kaucewa wata akuya, wanda hakan ya haddasa ƙwacewar motar ta faɗi nan take.
Ya ƙara da cewa, wannan kaucewa akuyar da direban motar ya yi ne ya kai ga faruwar wannan hatsari da ya kai ga mutuwar waɗannan bayin Allah.
A cewarsa tunin aka kai waɗanda suka Jikkata babban asibitin Ringin don kula da lafiyar su yayin da su kuma waɗanda suka rasu aka miƙa gawarwakin wasu ga iyalan su don musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya shimfiɗa.
Daga nan sai ya gargaɗi masu abubuwan hawa da su riƙa kula da ƙa’idojin tuƙin kana su rage gudun wuce kima don kaucewa faruwar mummunan haɗari.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link