AFCON 2025: Ƙasashe 5 Da Za Su Iya Lashe Gasar Nahiyar Afirka
[ad_1]
A ranar Lahadi aka fara gasar Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) ta 2025 a Birnin Rabat, da ke Ƙasar Morocco, inda mai masaukin baƙi ta doke Comoros da ci 2–0, wanda hakan ya sa ta fara gasar da ƙafar dama.
Brahim Díaz da Ayoub El Kaabi ne suka zura ƙwallayen biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, lamarin da ya nuna irin ƙwarewa da ƙarfi da tawagar ke da shi, wanda ya sa ake kallon su a matsayin waɗanda za su iya lashe gasar.
- Xi Ya Taya Jose Antonio Kast Murnar Lashe Zaben Shugaban Chile
Ƙasashe 24 ne suka samu gurbin zuwa gasar ta bana, inda ake sa ran za a buga wasanni masu zafi cike da armashi.
Daga cikin ƙasashen da za su fafata akwai manyan ƙasashe irin su Morocco, Masar, Senegal, Aljeriya, Nijeriya, Côte d’Ivoire, Kamaru, Afirka ta Kudu, DR Congo, Mali, Tunisiya, da sauran ƙasashe kamar Comoros, Sudan, Angola, Zambia, Uganda, da Benin.
Manyan Ƙasashen Da Ake Hasashen Za Su Iya Lashe Gasar Ta Bana
1. Maroko – A matsayinta na mai masaukin baƙi na gasar, kuma ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka mafi ƙarfi a duniya, Morocco ta fara gasar AFCON ta 2025 a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da ake shakka. Samun gogaggen mai horaswa, samun goyon bayan magoya baya a gida, da kuma haziƙan ’yan wasa, ya sa sun zama sahun gaba wajen neman lashe gasar. Tawagar tana fatan kawo ƙarshen dogon lokaci da ta shafe ba tare da lashe gasar ba.
2. Misira – Masar, wadda ta lashe AFCON sau bakwai a tarihin gasar, ta shiga gasar da tarihi da kuma dogaro da fitaccen ɗan wasan nan, Mohamed Salah, wanda ke da burin jagorantar Pharaohs zuwa nasara.
Tarihi da ƙwarewarsu a wannan gasa ya sa suka zama barazana ga kowace ƙasa.
3. Senegal – Zakunan Teranga, zakarun AFCON na 2021, har yanzu suna daga cikin manyan ƙasashen Afirka. Suna da tawagar ƙwararrun ‘yan wasa, suna buga ƙwallo cikim sauri da tsari mai kyau, wanda hakan ya sa abokan hamayya ke shakkarsu.
4. Aljeriya – Ana musu kirari da masu abun ban mamaki. Ko da yake Aljeriya ta fuskanci ƙalubale a ’yan shekarun baya, amma duk da haka har yanzu tana da ’yan wasa masu fasaha da gogewa.
5. Najeriya – A gefe guda kuma, Nijeriya na da Super Eagles, wadda ke da ‘yan wasa masu cike da basira da ƙarfi a gaba. Nijeriya ta zama barazana a Afrika a baya-bayan nan duna da irin jajirtattun ‘yan wasan da ta haɗa da kuma gogaggen mai horaswa.
Sauran Ƙasashen da Za Su Iya Ba Da Mamaki
Ƙasashe irin su Côte d’Ivoire (zakarun gasar bara), Kamaru, Tunisiya, Afirka ta Kudu, Mali, da DR Congo su ma na da ƙwarewa da haziƙan ’yan wasa da za su iya taka wa manyan ƙasashe burki idan suka yi amfani da damar da suka samu.
Gasar AFCON ta 2025 na shirin zama ɗaya daga cikin gasar da za ta fi ɗaukar hankali duba da irin tanadi da shirin da masu masaukin baƙi suka yi.
Gasar ta haɗa manyan ƙasashen da suka shahara a tarihin ƙwallon ƙafar Afirka da kuma ƙasashe masu tasowa da ke shirin nuna bajintarsu. Duk da cewa Morocco na da fifiko saboda kasancewarsu masu masauki baƙi da kyakkyawan tsari, ƙasashe irin su Masar, Senegal, Nijeriya, da Côte d’Ivoire sun yi shiri na musamman domin fafatawa wajen lashe kofin na bana.
Masoya ƙwallon ƙafa a faɗin Afirka na sa ran ganin gasa mai cike da tsari, tarihi da abubuwan tunawa.






[ad_2]
Source link