Kasafin Kuɗin Tinubu Na 2026 Tarkon Bashi Ne, Ba Gyara Ba — ADC

[ad_1]

Jam’iyyar ADC ta yi kaca-kaca da kasafin kudin Shugaba Bola Tinubu na 2026, inda tace tarkon bashi ne kawai aka ɓoye a matsayin gyara, tana gargadin cewa kasafin ya dogara ne da yawan rancen kuɗi da hasashen kuɗaɗen shiga marasa tushe wanda zai ƙara jinginar da makomar Nijeriya da kuma ƙara wargaza tattalin arziƙin ƙasar.

ADC, a cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labaranta na Ƙasa, Bolaji Abdullahi ya fitar a ranar Litinin, ta ce kasafin kuɗin ya ƙunshi abin da ta bayyana a matsayin tsarin rashin sanin tattalin arziki, da hasashen da ba su da tushe wanda gwamnatin Tinubu ta saba.

A ranar Juma’a, Shugaba Tinubu ya gabatar da kudirin kasafin kudin 2026 na tiriliyan ₦58.18 ga Majalisar Dokoki ta Kasa, yana mai nuna kyakkyawan fata game da farfadowar tattalin arziki a hankali da kuma yin alkawarin kara tsaurara matakan kula da harkokin kudi.

Yayin da yake gabatar da kasafin kuɗin a gaban taron hadin gwiwa na Majalisar Dattawa da Wakilai, Shugaban ya ce an tsara kudurin ne don ci gaba a kan sabbin gyare-gyaren tattalin arziki, sake gina kwarin gwiwa, da samar da fa’idodi masu yawa ga ‘yan Nijeriya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *