An yi garkuwa da masu zuwa Maulidi 28 a Filato
[ad_1]
’Yan bindiga sun sace mutane 28 da ke hanyarsu ta zuwa taron Maulidi a Zak da ke a Jihar Filato.
Maharan su yi garkuwa da matafiyan ne a daren Lahadi a kauyen Zak, da ke gundumar Bashar, ta Ƙaramar Hukumar Wase ta jihar.
Wani jagoran matasa a Wase, Shafi’i Sambo, ya ya shaida wa wakilinmu ya wayar tarho cewa wadanda aka sace sun haɗa da maza, mata da yara.
Shafi’i Sambo ya ce, ’ya’ya sarakuna biyu da wani jagoran addini da ke jagorantar tafiyar suna cikin wadanda aka sace.
Ya ce, “Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8 na dare a lokacin da suke kan hanyarsu zuwa Sabon Layi domin taron. Lokacin da ’yan bindigar suka tare motar da ke ɗauke da matafiyan a wajen kauyen, suka tafi da dukkan matafiyan ciki har da yara, suka bar motar a wurin.
“Da safiyar Litinin ne wasu matafiya da ke bi ta hanyar suka ga motar, wacce ta mallaki shugaban kauyen Zak, a ajiye a hanya.
“A yayin bincike ne al’umma suka gano cewa motar da ke dauke da matafiyan ce aka ajiye,” in ji Shafi’i.
Wani mazaunin garin Bashar, Ibrahim Musa, ya ce har yanzu ba a san inda aka kai waɗanda aka sace ba.
A cewarsa, an sace mutanen ne a hanyarsu daga kauyen Zak zuwa yankin Sabon Layi domin halartar taron Maulidi da aka shirya gudanarwa a ranar Lahadi.
Shafi’i Sambo ya ce duk ƙoƙarin gano inda aka kai mutanen bai yi nasara ba, yana mai ƙara da cewa an sanar da jami’an tsaro game da lamarin.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Alabo Alfred, ya ce suna binciken rahoton lamarin a lokacin da aka tuntube shi.
Wakilinmu ya ruwaito cewa garkuwa da mutane, ta’addanci da satar shanu sun yi ƙamari a yankin Wase baki ɗaya, inda mazauna ke kira ga jami’an tsaro da su kawar da miyagun da ke addabar yankin.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link