Ƙungiyar NUT Ta Koka Kan Ƙarancin Malamai 194,000 A Nijeriya
[ad_1]
Yayin da duniya ke bikin Ranar Malamai ta Duniya ta 2025, ƙungiyar malamai ta ƙasa, Nigeria Union of Teachers (NUT), ta koka kan matsanancin ƙarancin malamai da kuma cika alƙawuran da gwamnati ta yi na inganta jin daɗin malamai.
Shugaban ƙungiyar, Comrade Audu Titus Amba, ya bayyana haka ne a wurin bikin da aka gudanar a Eagle Square, Abuja, cewa ƙididdigar hukumar UBEC ta nuna ana da ƙarancin malamai 194,876 a makarantun firamare na gwamnati a faɗin Nijeriya. Ya ce wannan matsala na barazana ga ingancin koyarwa da nasarar manufar SDG 4 ta ilimi mai nagarta ga kowa.
Amba ya bayyana takaicinsa cewa tun daga shekarar 2020, yawancin alƙawuran da aka yi kan ƙarin alawus ko jin fannin jin daɗi ga malamai ba a cika su ba, sai dai tsawaita shekarun ritaya zuwa shekara 65 da jihohi 22 da FCT suka aiwatar. Ya kuma nuna damuwa kan rashin aiwatar da sabon albashin ƙasa na 2024, inda ya ce jihohi 10 ba su cika ba, yayin da jihohi 4 ba su fara ba kwata-kwata.
Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohi su ɗauki mataki cikin gaggawa wajen ɗaukar ƙarin malamai, da cika alƙawuran walwalar malamai da kuma sa aikin koyarwa ya zama abin sha’awa ga matasa.
Bikin, wanda taken sa shi ne “Sake Fasalin Koyarwa a Matsayin Sana’ar Haɗin Kai,” ya haɗa da bayar da lambar yabo ga gwamnonin jihohi da malamai da suka fi fice.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp
[ad_2]
Source link