NAFDAC ta lalata magungunan jabu na N15bn a Oyo

[ad_1]



Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna a Najeriya (NAFDAC) a ranar Alhamis ta lalata magunguna da kayayyakin jabu, da wa’adin aikinsu ya ƙare da marasa inganci, da jabun magunguna da darajarsu ta kai Naira biliyan 15 a garin Ibadan na Jihar Oyo.

Darakta-Janar ta Hukumar NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta sanar da hakan a lokacin da aka lalata magungunan a Ibadan, babban birnin jihar.

Adeyeye wanda Daraktan bincike da tabbatar da doka na NAFDAC, Martins Iluyomade ya wakilta, ya ce hukumar ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da cewa abinci, magunguna, kayan kwalliya, na’urorin likitanci, sinadarai da abubuwan sha suna da lafiya, masu inganci kuma masu amfani ga ɗan Adam.

“Babu shakka cewa, magunguna wani muhimmin al’amari ne ga Hukumar NAFDAC, kuma hukumar ta kafa tsauraran ƙa’idoji da suka shafi bayar da lasisi da sayarwa da rarraba kayayyakin magunguna.

“Kayayyakin da muka lalata a ranar Alhamis sun haɗa da na magungunan da wa’adinsu ya ƙare da na jabu da marasa tsari da marasa rijista da kuma haramtattun magunguna irin su: Analgin da Cocodamol da codeine syrup syrup da tramadol da oɗytocin da nau’ukan allurar rigakafi iri-iri.

“Kimanin darajar waɗannan kayayyakin da aka lalata a ya kai Naira biliyan 15.”

Ta bayyana cewa, lalata waɗannan kayayyakin zai kawar da barazanar sake shiga kasuwannin Najeriya.

Shugaban Hukumar ta yaba da goyon bayan da ’yan sanda, sojojin Nijeriya, ma’aikatar kula da harkokin gwamnati, NDLEA da jami’an tsaron farin kaya da na Ciɓil Defence da kuma Ƙungiyar harhaɗa magunguna ta Najeriya da dai sauransu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *