Kwankwaso: ADC Ta Zargi Shirin Rikita Jam’iyyar, Ta Zargi Gwamnati Da Matsa Wa INEC Lamba

[ad_1]

Jam’iyyar ADC ta zargi Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin jam’iyyar APC da kokarin haddasa rikici a cikin jam’iyyar, bayan sauya sheƙar Rabiu Musa Kwankwaso zuwa ADC.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Kasa, Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce ana kara matsa wa shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Joash Ojo Amupitan, lamba domin ya tsoma baki cikin tsarin shugabancin cikin gida na jam’iyyar.

  • Alkaluman PMI Na Sin Sun Karu Da Kaso 50.4 Bisa Dari A Watan Maris
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Wajen Biki A Kaduna, Sun Kashe Mutane 13

ADC ta kuma yi zargin cewa wata wasika mai dauke da kwanan wata 28 ga Maris, 2026, da wasu manyan lauyoyi, SAN suka rubuta a madadin wani mutum da ta bayyana a matsayin tsohon mamba da aka kora, ana amfani da wannan ikirarin wajen matsa wa INEC lamba domin ta soke wasu muhimman matakai da shugabancin jam’iyyar ya dauka.

A cewar jam’iyyar, wasikar na kokarin tilasta wa hukumar zaben, fassara hukuncin Kotun Daukaka Kara ta yadda za a sauya tsarin jam’iyyar kafin kotu ta yanke hukunci na karshe kan lamarin.

Har ila yau, ADC ta yi zargin cewa wasikar ta kunshi barazana ga shugaban INEC tare da bukatar a janye wasu matakan jam’iyyar, ciki har da amincewa da wasu jami’ai.

Jam’iyyar ta karyata ikirarin Nafiu Bala Gombe, inda ta bayyana shi a matsayin tsohon mamba wanda ya yi murabus sannan daga bisani aka kore shi, tana mai cewa bai taba zama shugaban jam’iyyar na kasa ba.

Haka kuma, ADC ta danganta wannan lamari da abin da ta kira matsin lamba na siyasa bayan sauya sheƙar Kwankwaso kwanan nan, wanda ta ce ya kara wa jam’iyyar farin jini da goyon baya.

A karshe, jam’iyyar ta bukaci INEC da ta kasance mai tsaka-tsaki tare da bin tanade-tanaden kundin tsarin mulki, tana gargadin kada a yi yunkurin tsoma baki cikin harkokin cikin gida na jam’iyyar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *