Sin Da Pakistan Sun Ba Shawarwari Biyar Kan Maido Da Zaman Lafiya A Yankin Gulf Da Gabas Ta Tsakiya

[ad_1]

A yau Talata, 31 ga watan Maris, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya tattauna da mataimakin firaministan Pakistan kuma ministan harkokin wajen kasar, Mohammad Ishaq Dar a birnin Beijing. Sassan biyu sun yi musayar ra’ayoyi game da halin da ake ciki a yankin Gulf da kuma Gabas ta Tsakiya, kana suka gabatar da wasu muhimman shawarwari kamar haka: Na farko, a dakatar yake-yake ba tare da bata lokaci ba. Na biyu, a fara shirin tattaunawa kan zaman lafiya ba da jimawa ba. Na uku, a tabbatar da kiyaye abubuwan da ba su shafi soja ba. Na hudu, a tabbatar da kiyaye tsaron hanyoyin jiragen ruwa. Kana na biyar, a tabbatar da dora kundin dokokin Majalisar Dinkin Duniya a gaba da komai. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *