Yadda Kungiyar Ma’aikatan Lafiya Ta Shafe Sama Da Wata 2 Tana Yajin Aiki
[ad_1]
Batun yajin aikin Kungiyar Ma’aikatan Lafiya (JOHESU) da Yaƙi-ci-yaƙi-cinyewa, ya damalmala harkokin kiwon lafiya, inda lamarin ya shafe sama da kwanaki 74, babu wani sashi na ma’aikatan lafiya a cibiyoyin lafiya na gwamnatin tarayya da lamarin bai taɓa ba.
A ranar 22 ga watan Janairun 2026, Sakataren Kungiyar JOHESU na Kasa, Kwamared Martin Egbanubi ya fitar da sanarwa game da zaman da ya gudana tsakanin tawagar gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin karamin ministan lafiya, Dr. Iziaq Adekunle Salako da kuma shugaban JOHESU, Kwamared Kabiru Minjibir tare da rakiyar sakataren kungiyar TUC domin ganin an shawo kan lamarin a Abuja.
- Yawan Kudaden Da Baki Suka Kashe A Sin Ya Karu A Shekarar Bara
- Yawan Kudaden Da Baki Suka Kashe A Sin Ya Karu A Shekarar Bara
Gwamnatin tarayya ta gabatar da shawara a matsayin martani ga wadda JOHESU ta gabatar a ranar 20 ga Janairu, 2026. JOHESU ta nuna cewa, za ta yi duba kan shawarar amma tana buƙatar a turo shawarar a hukumance domin tabbatarwa.
A yayin taron, duka ɓangarorin biyu, sun amnince cewa, gwamnatin tarayya za ta rubuto shawararta ga JOHESU a hukumance, ita kuma ta duba shawarar, sannan ta tattauna a matakin da ya dace.
An ɗage taron zuwa wani lokaci, domin bayar da damar aiwatar da shawararwarin da aka gabatar.
in ba a manta ba, JOHESU dai na gwagwarmaya ne domin ganin a aiwatar da tsari da dokar da aka tanada game da sabunta tsarin albashin na CONHESS wanda Ma’aikatan Jinya, Masu hada Magunguna, Masu aiki a Dakunan Gwaje-gwaje, Masu Jinya ta motsa jiki (Physiotherapists), Masu daukar Hoton Jiki (Radiographers), da sauran kwararru da ma’aikatan tallafi a ɓangaren lafiya ke ƙarƙashi, kamar yadda gwamnatin ta aiwatar da tsarin albashi na CONMESS ga Likitoci da Likitocin Haƙora.
“Mun shiga yajin aiki ne musamman domin neman gyara da daidaita Tsarin Albashin Ma’aikatan Lafiya (CONHESS). Tun daga shekarar 2014, albashin likitoci (a karkashin CONMESS) an yi masa gyara sau da dama, yayin da sauran ma’aikatan lafiya aka yi watsi da su sama da shekaru goma. Muna neman adalci da daidaito a ɓangaren lafiya,” in ji sanarwar
[ad_2]
Source link