Abba Kabir zai samu wa’adi na biyu a 2027 — Ganduje

[ad_1]



Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya tabbatar wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, cewa zai yi nasara a zaɓen gwamna na 2027, yana mai cewa jam’iyyar APC za ta ba shi cikakken goyon baya domin samun wa’adi na biyu.

Ganduje ya faɗi hakan ne a Kano yayin tarbar Abba Kabir Yusuf da ya sake komawa APC, inda ya bayyana komawar tasa a matsayin tarihi kuma abin alheri ga jam’iyyar da jihar baki ɗaya.

“Za ka yi nasara a wa’adi na biyu a 2027. Mun tattauna da duk masu sha’awar neman takara, kuma sun amince za su mara maka baya,” in ji Ganduje.

Ya ce komawar Abba tamkar dawowa gida ne, yana mai tunatar da cewa gwamnan na daga cikin waɗanda suka kafa APC tun farko, kafin rikice-rikicen siyasa su raba su.

Ganduje ya kuma bayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin ɗan siyasar ci gaba wanda salon jagorancinsa ya dace da akidar APC, yana mai jaddada cewa a bisa tsarin jam’iyyar, gwamnan shi ne jagoran APC a Jihar Kano.

Haka nan ya tabbatar masa da samun adalci da cikakkiyar karɓuwa a cikin jam’iyyar, tare da bayyana kwarin gwiwar cewa APC za ta samu gagarumar nasara a zaɓuka masu zuwa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *