Mataimakin Gwamna Yusuf Bai Halarci Taron Sauya Sheƙar Maigidansa Zuwa APC Ba

[ad_1]

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Abdulsalam Gwarzo, bai halarci taron sauya shekar maigidansa, gwamna Yusuf ba zuwa jam’iyyar APC ba a ranar Litinin, wanda hakan ke nuna gagarumin saɓani a siyasar jihar kafin babban zaben 2027.

Gwamnan ya sanar da sauya shekarsa a wani taron da aka gudanar a babban dakin taro na ‘Coronation Hall’ da ke gidan gwamnatin Kano.

  • Ganduje Ya Koma Abuja Daga Landan, APC Na Shirye-shiryen Karɓar Gwamnan Kano
  • Yanzu-yanzu: Kwamishinan Ci Gaban Matasa, Mustapha Kwankwaso, Ya Yi Murabus

Amma duk da sauya shekarsa, Gwamna Yusuf ya bayyana a wurin bikin sanye da riga mai launin fari ta Kwankwasiyya da kuma hula ja, inda hakan ke nuna cewa, har gobe kama yana tare da akidar Kwankwasiyya.

A jawabinsa ga taron, gwamnan ya ce, ya ɗauki shawarar shiga APC ne don amfanin jama’ar jihar Kano, bayan tattaunawa mai zurfi da kuma yin nazari sosai kan buƙatun jihar na gaba. Duk da haka, rashin bayyanar mataimakinsa a wurin taron, na nuna, rabuwar kawuna a tsakanin su.

“Yau tarihi ne, ba wai kawai ga wannan gwamnati ba, har ma ga dukkan mutanen Kano nagari,” in ji Yusuf.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *