Gwamnan Kano Abba Kabir ya koma APC

[ad_1]



Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya koma jam’iyyar APC mai mulki, bayan kammala ficewarsa daga jam’iyyar NNPP da aka zaɓe shi a ƙarƙashinta.

Wannan dai ya kawo ƙarshen raɗe-raɗin aka riƙa yi na sauya sheƙar gwamnan zuwa jam’iyyar mai mulki a ƙasar a wani yanayi da masu sharhi suka bayyana a matsayin shirye-shiryen tunkarar Zaɓen 2027.

Tuni dai rahotanni daga gidan gwamnati suka nuna cewa yadda kafa manyan alluna a sassa daban-daban na birnin Kano, waɗanda ke ɗauke da hoton Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da kuma wasu jiga-jigan jam’iyyar APC, ciki har da tsohon gwamnan jihar kuma tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Haka kuma, an sauya tutocin jam’iyyar NNPP da na APC, tare da ƙawata babban ɗakin taro na gidan gwamnatin jihar da hotunan Shugaba Tinubu da na Gwamna Abba Kabir Yusuf, duk ɗauke da tambarin jam’iyyar APC.

Tun a ranar Lahadin da ta gabata Aminiya ta ruwaito cewa ana sa ran gwamnan zai sanar da komawarsa jam’iyyar APC a hukumance a wannan Litinin ɗin.

A baya-bayan nan, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya danganta ficewarsa daga NNPP da rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyar, yana mai cewa ya yanke shawarar sauya sheƙa ne domin amfanin Jihar Kano da kuma al’ummar da yake jagoranta.

Masu lura da al’amuran siyasa na ganin wannan sauyi na iya sauya fasalin siyasar Kano da ma Arewa gaba ɗaya, yayin da ake sa ran APC za ta ƙara ƙarfafa matsayinta a jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *