An kashe manoma 6 a Filato
[ad_1]
Aƙalla manoma shida ne suka mutu, sannan ɗaya ya jikkata a wani sabon harin da aka kai a wasu ƙauyukan Foron da Gero da ke karamar hukumar Jos ta Kudu da Barikin Ladi a Jihar Filato.
A cewar shugaban Ƙungiyar matasa ta Berom Youth Moulder-Association (BYM) na ƙasa, Solomon Dalyop wasu mahara sun kai hari a wurin da ake haƙar ma’adinai a yankin Gero.
Ya ce, harin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:34 na safe, inda aka kashe mutane biyar, ɗaya kuma ya jikkata. Maharan sun buɗe wuta kan masu haƙar ma’adinai, lamarin da ya tilasta musu tserewa.
A wani lamari makamancin haka, kakakin Ƙungiyar ta BYM Rwang Tengwong a ranar Alhamis ya ce wasu ’yan bindiga sun kashe mutum ɗaya a kusa da unguwar Foron a Ƙaramar hukumar Barikin Ladi.
Ya ce, “A yayin harin, Mista Ayuba Pam Choji, mai shekara 44, an kashe shi da wuƙa, wanda ya tsira kuma, wanda suke tafiya a kan babur ɗaya tare da marigayin, ya bayyana cewa, kwatsam maharan sun fito daga maɓoya, suka far musu haka kawai.
Ya ce, wani ganau ya kuma bayyana cewa, maharan a baya suna zaune a kewayen Bisichi, waɗanda ake zargin sun yi barazana da kuma bayar da wa’adin ficewa daga yankin kafin ranar 7 ga watan Janairu, 2026, inda ya ƙara da cewa, bayan harin an ce an ga maharan suna guduwa zuwa yankin Bisichi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link