Sin: Amurka Ta Dade Tana Zama Jagorar Haddasa Fitina A Bangaren Sadarwar Intanet
[ad_1]
Amurka ta dade tana zama jagorar haddasa fitina a bangaren sadarwar intanet. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fada a yau Litinin cewa, Amurka ta kasance tana kai hare-hare ta shafin intanet da kuma kawo cikas ga muhimman kayayyakin aiki na kasar Sin tun ma kafin a fara samun ci gaban fasahar kirkirarriyar basira ta AI.
An ba da rahoton cewa, ma’aikatar yaki ta Amurka tana tattaunawa da manyan kamfanonin AI game da hadin gwiwa don yin amfani da fasahar AI wajen gudanar da bincike da tattaro bayanai kai-tsaye kan hanyoyin samar da wutar lantarki na kasar Sin, da ababen more rayuwar al’umma da hanyoyin sadarwar intanet masu muhimmanci don gano wasu kura-kurai da za a iya amfani da su a kowane irin rikici da zai taso.
Mai magana da yawun ma’aikatar Mao Ning ta ce, har ma gwamnatin Amurka ta bukaci manyan kamfanonin fasaha da su yi wa Amurka aiki kai-tsaye a kan wadanda ake son fatattaka a fagen siyasar yanki, da siyasa da sha’anin soja, matakin da ke da mummunan tasiri a duniya. Bangaren kasar Sin ya bayyana matukar damuwarsa ga bangaren Amurka baro-baro a fili ta hanyoyi da dama, kuma zai tabbatar da tsaron shafin intanet na kasar Sin tare da daukar dukkan matakan da suka dace. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link