Wang Yi Ya Tattauna Da Ministan Harkokin Wajen Iran Da Na Faransa Da Na Oman Ta Wayar Tarho
[ad_1]
Ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya tattauna da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ta wayar tarho a yau 2 ga wannan wata.
Araghchi ya bayyana cewa, kasar Amurka ta kaddamar da yaki ga kasar Iran a karo na biyu yayin da ake kan shawarwari a tsakaninsu. Bangarorin biyu sun riga sun samu ci gaba a yayin shawarwarin, amma matakin kasar Amurka ya saba wa dukkan dokokin kasa da kasa, da keta hakkin kasar Iran. Babu shakka kasar Iran ta tabbatar da tsaron kanta.
Wang Yi ya jaddada matsayin Sin kan yanayin kasar Iran, Sin ta nuna goyon baya ga kasar Iran wajen tabbatar da ‘yancin kasar da kiyaye martabar yankunanta da mutuncin al’ummar kasar, da kuma tabbatar da moriyarsu bisa dokoki baki daya.
Wang Yi ya bayyana cewa, Sin ta riga ta kalubalanci kasar Amurka da Isra’ila da su dakatar da matakin na soja cikin hanzari, da magance tsanantar halin da ake ciki, da kuma magance fadada yakin zuwa dukkan yankin Gabas ta Tsakiya.
A wannan rana, Wang Yi ya kuma tattauna da ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Noël Barrot ta wayar tarho, inda ya yi fatan kasar Faransa za ta dauki matsayi mafi dacewa, da kiyaye maido da zaman lafiya, da yin kokari tare da kasar Sin wajen sa kaimi ga sassauta yakin da kuma tabbatar da ka’idojin kiyaye huldar dake tsakanin kasa da kasa baki daya.
Hakazalika, Wang Yi ya tattauna da ministan harkokin wajen kasar Oman Sayyid Badr bin Hamad Albusaidi ta wayar tarho, inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana kokarin taka muhimmiyar rawa wajen daidaita batun cikin adalci a kwamitin sulhun MDD, da neman shimfida zaman lafiya da dakatar da yakin baki daya. (Zainab Zhang)
[ad_2]
Source link