Kasar Sin Za Ta Yi Aiki Da Sauran Kasashe Wajen Karfafa Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya
[ad_1]
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasashen duniya wajen yin kokari sosai don karfafa zaman lafiya da riga-kafin afkuwar yaki, da kuma warware matsala ta hanyar tattaunawa da yin shawarwari, ta yadda za a kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki daya.
Yayin da take amsa tambaya game da hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran, a taron manema labarai na yau da kullum, mai magana da yawun ma’aikatar Mao Ning ta ce, Sin ta damu matuka game da halin da ake ciki a yanzu, kuma tana matukar adawa da yin amfani da karfin tuwo a huldar kasa da kasa, wanda ya saba wa ‘yancin kai da tsaron sauran kasashe.
Mao ta kara da cewa, babban aikin da ya fi daukar hankali a yanzu shi ne dakatar da matakan soji nan take da kuma riga-kafin karuwar tashe-tashen hankula da barkewar rikice-rikice.
Mao ta ce Amurka da Isra’ila sun kaddamar da hare-haren soji kan Iran ba tare da izinin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ba, wanda ya saba wa dokokin kasa da kasa, kana ta kara da cewa, kasar Sin ta nuna matukar damuwarta kan yadda rikicin ke shafar kasashe makwabta. Kasar Sin ta yi imanin cewa, kamata ya yi a mutunta ‘yancin kai, tsaro, da martabar yankunan kasashen yankin Gulf. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link