2027: PDP Za Ta Yi Duk Abin Da Ya Dace Domin Ceto Dimokiraɗiyyar Nijeriya – Jigo A PDP
[ad_1]
Mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa mai kula da shiyyar Kudu–Maso-Kudu, Emmanuel Ogidi, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta ɗauki matakai masu ƙarfi domin kare dimokiraɗiyyar Nijeriya, tare da ƙarfafa haɗin kan ƙasa a gabanin zaɓen 2027.
Ogidi ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Lahadi, inda ya ce PDP na shirin sake tsayawa tsaye a matsayin jam’iyyar adawa mai ƙarfi, wadda za ta iya daidaita tafiyar mulki da kuma kawo ci gaba ga al’ummar ƙasa.
- Gwamna Lawal Ya Fara Ganawa Da Manyan Jiga-jigan PDP A Zamfara
- Zamfara: PDP Ta Yaba Wa Kotun Abuja Kan Nasarar Da Ta Samu
Ya amince da cewa jam’iyyar na fuskantar wasu matsaloli na cikin gida, amma ya jaddada cewa waɗannan ƙalubalen ba za su hana PDP cika aikinta na kare dimokiraɗiyya da muradun jama’a ba. A cewarsa, jam’iyyar ba za ta ci amanar ‘yan Nijeriya da ke kallonta a matsayin ginshiƙin adawa a ƙasar nan ba.
Jigon na PDP ya ƙara da cewa jam’iyyar za ta buɗe ƙofofin tattaunawa da sauran masu ruwa da tsaki a fagen siyasa, ciki har da wasu daga jam’iyyar APC, domin haɗa kai wajen kare dimokiraɗiyyar ƙasa, inda ya yi gargaɗin cewa sakaci kan wannan batu na iya jefa Nijeriya cikin manyan matsaloli.
A ƙarshe, Ogidi ya ce babban burin PDP a zaɓen 2027 shi ne tabbatar da dimokiraɗiyya mai ƙarfi, ƙarfafa haɗin kan ƙasa da kuma inganta tsarin siyasa a faɗin Nijeriya.
[ad_2]
Source link