Ana zargin cutar Kwalara ta kashe yara 10 a Taraba
[ad_1]
Akalla yara fiye da 10 sun mutu sakamakon ɓarkewar cutar da ake zargin kwalara ce a garin Chanchangi da ke karamar hukumar Takum a jihar Taraba.
Aminiya ta samu labarin cewa kimanin kwanaki uku da suka gabata wasu yara masu shekaru tsakanin hudu zuwa goma sun fara amai da gudawa a garin.
An tattaro cewa cikin kwanaki biyu kacal fiye da yara goma sun riga mu gidan gaskiya, lamarin da ya haifar da zargin barkewar kwalara a yankin.
Jami’an lafiya daga ma’aikatar lafiya ta jihar da kuma sashen lafiya na karamar hukumar Takum sun isa yankin domin daukar matakan dakile yaduwar cutar.
Kwamishinan Lafiya na jihar Taraba, Dakta Bodiya Buma, bai dauki kira ba kuma bai amsa sakon rubutu da na WhatsApp da wakilinmu ya tura masa kan barkewar cutar da ake zargi ba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link