Masanin Angola: Manufar Soke Harajin Kwastam Za Ta Bude Sabon Babi Na Raya Dangantakar Sin Da Afirka
[ad_1]
Wani masani na jami’ar Agostinho Neto ta kasar Angola Paixão José ya rubuta sharhi mai taken “manufar soke harajin kwastam za ta bude sabon babi na raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka” a shafin intanet na jaridar Correio da Kianda a kwanakin baya.
A cikin sharhinsa, ya ce kasar Sin za ta aiwatar da manufar soke harajin kwastam a dukkan fannoni ga kasashen Afirka 53 da suka kulla dangantakar diflomasiyya da ita daga ranar 1 ga watan Mayun shekarar 2026, inda hakan zai karfafa matsayin Sin na abokiyar cinikayya mafi girma a nahiyar Afirka, kana zai sa kaimi ga shigar da kayayyakin Afirka ciki har da kofi, da kayan masaka, ma’adanai, man fetur, amfanin gona da sauransu zuwa kasuwar kasar Sin, wadda ta hakan za a inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa.
Tun daga farkon karni na 21, kasashen Afirka da kasar Sin sun kiyaye raya dangantakarsu a fannonin cinikayya, da ayyukan more rayuwa, da masana’antun samar da kaya, da kimiyya da fasaha, da harkokin diflomasiyya da sauransu, yanzu an kafa huldar tattalin arziki a tsakaninsu bisa tushen yarjejeniyoyin samun moriyar juna da raya hadin gwiwarsu na dogon lokaci.
Aiwatar da manufar soke harajin kwastam a kasashen Afirka ta kasance wani muhimmin aiki na raya hadin gwiwa da samun moriyar juna a tsakanin Sin da Afirka, inda lamarin ya yi alamanta cewa, hadin gwiwar Sin da Afirka ya shiga sabon mataki, da inganta karfin kasashen Afirka kan cinikayyar duniya baki daya. (Zainab Zhang)
[ad_2]
Source link