Wike Ya Ƙwace Filaye 485 A Abuja Kan Rashin Cika Ƙa’idojin Mallaka

[ad_1]

Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya soke takardun filaye kimanin 485 a Abuja, bayan gaza tantancewarsu da aka yi a hukumance.

Hukumar Kula da Babban Birnin Tarayya Abuja (FCTA), ta ce; waɗanda abin ya shafa ba su yi bincike na gaskiya ba a kan filayen, wanda a ƙarshe aka kuma tabbatar da cewa na bogi ne. An bayar da wannan sanarwa ce a cikin sanarwar da Sashen Kula da Filaye da Hukumar Kula da Harkokin Ƙasa ta Abuja (AGIS), suka bayar.

  • Rikicin Wike Da Fubara Na Ƙara Tsananta, Tinubu Ya Sake Shiga Tsakani
  • HOTUNA: Wike Ya Buɗe Gidan Rediyo Don Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu A Ribas

Sanarwar ta bayyana cewa, ministan ya amince da soke filayen da aka gaza tantancewa, sannan kuma za a cire takardun da aka soke daga rumbun adana bayanai. Ya ƙara da cewa, an ɗauki wannan matakin ne ba tare da sake wata sanarwa ba.

Takardun da abin ya shafa, sun ratsa yankuna da dama da garuruwan da ke cikin birni. A Ƙaramar Hukumar Bwari, wuraren da abin ya shafa sun haɗa da tsarin faɗaɗa ƙauyen Ushafa. A cikin Ƙaramar Hukumar Babban Birnin Tarayya (AMAC), sun haɗa da Kurudu-Jikwoyi, faɗaɗa yankin Karu, Nyanya Phase Iɓ, Jikwoyi, Sabon Lugbension da Lugbe Igbe. Sai kuma Kuchiyako a cikin Kuje.

Ƙasar da ke cikin FCT, ta kasance mallakin gwamnatin tarayya a ƙarƙashin dokar amfani da ƙasa ta 1978, kuma dole ne Ministan FCT ya ba da laƙabi, kuma a rubuta shi a AGIS. Matakin na baya-bayan nan yana da nasaba da jabu da rashin sahihanci, maimakon rashin biyan kuɗi ko wani abu mai kama da wannan, in ji gwamnatin.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *