Ana zargin ’yan sakandire sun kashe ɗalibi da duka a Yobe

[ad_1]



Ana fargabar cewa wani ɗalibin aji shida (SS3) a Makarantar Sakandiren Kimiyya da Fasaha ta Gwamnati (GSTC) da ke Potiskum a Jihar Yobe, ya rasu sakamakon abin da ake zargin dukan da wasu abokan karatunsa suka yi masa.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a cikin harabar makarantar da ke ƙaramar hukumar Potiskum.

Binciken da Aminiya ta yi ya nuna cewa ana zargin wasu ɗalibai da suke aji ɗaya da kai masa hari, duk da cewa har yanzu ba a kammala tantance ainihin yadda lamarin ya faru ba.

Rahotanni sun ce an yi jana’izar marigayin a ranar da lamarin ya faru a garinsu Gadaka, da ke ƙaramar hukumar Fika a jihar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkarim, ya shaida wa Aminiya ta wayar tarho cewa rundunar ta fara bincike domin gano musabbabin mutuwar ɗalibin.

“Eh, mun samu rahoton lamarin, kuma tuni aka fara bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar ɗalibin,” in ji SP Abdulkarim.

Wani malami a makarantar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa mahukuntan makarantar sun miƙa wasu ɗalibai da ake zargi da hannu a lamarin ga ’yan sanda domin ci gaba da bincike.

“Mahukuntan makarantar sun miƙa ɗaliban da ake zargi ga ’yan sanda, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike,” in ji majiyar.

Da aka tuntubi Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare na Jihar Yobe, Farfesa Abba Idriss Adam, ya ce zai ba da cikakken bayani daga baya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *