Matashi ya mutu yayin ciro tukunyar gas a cikin rijiya

[ad_1]



Wani matashi mai kimanin shekaru 30 ya rasa ransa a yayin da yake ƙoƙarin ciro tukunyar gas daga cikin wata rijiya a Ƙaramar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ce ta tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da kakakinta, Saminu Abdullahi, ya fitar a ranar Litinin.

A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne a yammacin ranar Lahadi a unguwar Saulawa da ke garin Gwarzo, inda ofishin kashe gobara na yankin ya samu kiran gaggawa daga wani mazaunin yankin, Alhaji Dan Gwarzo.

Sanarwar ta bayyana cewa marigayin, mai suna Ashahabu Ubale, ya shiga rijiyar ne a ƙoƙarin ciro wata tukunyar gas da aka jefa ciki bayan ta kama da wuta.

Sai dai a yayin da ya shiga cikin rijiyar, tukunyar gas ɗin ta fashe, lamarin da ya rage ingantacciyar iskar oksijin (oxygen) a cikin rijiyar, wanda hakan ya sa suma.

Jami’an kashe gobara sun samu nasarar fito da shi daga rijiyar cikin wanda ba ya cikin hayyacinsa, inda aka bayan an garzaya da shi zuwa asibiti likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

A wani labarin kuma, rundunar kashe gobarar ta bayyana damuwa kan karuwar hatsarurrukan da suka dangancin nutsewa cikin ruwa a jihar.

Sanarwar ta ce a baya-bayan nan, wani matashi mai shekaru 18 mai suna Yusif Malam-Gwani ya nutse ya mutu a wani tafki da ke Bachirawa yankin Kwanar Madugu a Ƙaramar Hukumar Ungogo.

Haka zalika, wani yaro mai shekaru takwas, Abdussalam Ibrahim, ya rasa ransa bayan da ya faɗa cikin wata rijiya a Kofar Yamma da ke garin Karaye a Ƙaramar Hukumar Karaye.

Rundunar kashe gobarar ta shawarci jama’a da su ƙara yin taka-tsantsan, musamman wajen rufe rijiyoyi da sauran hanyoyin ruwa a buɗe, tare da lura da ƙananan yara domin kauce wa aukuwar irin waɗannan munanan lamurra.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *