Tsaro: Zanga-zanga Ta Ɓarke Biyo Bayan Sace Iyalai A Kaduna
[ad_1]
Mazauna garin Danhonu II da ke ‘New Millennium City’, karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, a ranar Litinin sun yi zanga-zanga kan yawaitar satar mutane da ‘yan bindiga ke cigaba da yi a yankin.
Masu zanga-zangar sun yi tattaki zuwa babban ofishin ‘yansanda na yankin ‘Millennium City’, inda suka toshe babbar hanyar shiga garin yayin da suke rera wakokin damuwa da kuma neman kai musu agajin gaggawa na jami’an tsaro.
- Dalilin Da Ya Sa Gwamnan Bauchi Ya Sauke Kwamishinan Tsaron Cikin Gida
- Ministar Wajen Madagascar Ta Yi Kiran Inganta Alakar Kasarta Da Kasar Sin Kafin Bikin Bazara Na Sinawa
Harin na baya-bayan nan, ya faru ne da misalin karfe 11:30 na dare a ranar Lahadi, inda ya shafi iyalan mutum biyu bayan ‘yan bindigar sun mamaye su.
Wadanda aka sacen sune Yahaya Yusuf, da matarsa Latifat Yusuf, da ‘ya’yansu maza, Abdulgafar da Abdulqudus.
Sauran sune, Hajiya Abdulrazak Jimoh da ‘ya’yanta biyu, wadanda ba a bayyana sunayensu ba a lokacin rubuta wannan rahoton.
[ad_2]
Source link