Ci Gaban Sin Zai Haifar Da Ci Gaban Afirka

[ad_1]

“Ci gaban kasashen duniya, ya kasance tushen ci gaban kasar Sin. Kana ci gaban Sin shi ma zai haifar da ci gaba a duniya.” Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba bayyana alakar dake tsakanin kasarsa da duniya kamar haka. To, idan mun takaita abubuwan da maganar ta shafa zuwa alakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, za mu ga hakan ma abun yake, wato ci gaban kasar Sin zai haifar da ci gaban kasashen Afirka. Hakika, ba wani abu mai wuya ba ne, idan ana son neman shaidu da za su tabbatar da gaskiyar maganar, ta hanyar karanta jawabin taya murnar sabuwar shekara da shugaba Xi Jinping ya gabatar, a kwanan nan, tare da gudanar da tsokaci a kansa.

Cikin jawabinsa, shugaba Xi ya ambaci nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin raya kasa. Cikin shekarar da ta shude, an sa ran cewa, jimillar GDPn kasar a mizanin duk shekara za ta kai kimanin kudin Sin Yuan triliyan 140, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 20, jimillar da ta shaida karuwar karfin kasar a fannin tattalin arziki. To, karanta bayanin ya sa ni tunawa da karuwar cinikin da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a bara. An ce, tun daga watan Janairu zuwa na Nuwamban shekarar 2025, darajar cinikin da aka yi tsakanin Sin da Afirka ta zarce dalar Amurka biliyan 300 a karon farko a tarihi, ta yadda kasar Sin ta kiyaye matsayinta na kawar ciniki mafi girma ta nahiyar Afirka wasu shekaru 16 a jere. Ban da haka, duk a cikin shekarar 2025, kasar Sin ta kulla yarjejeniyar hadin gwiwa, karkashin tsarin Ziri Daya da Hanya Daya, tare da karin kasashe, irinsu Kenya da Sudan ta Kudu. Kana ta kaddamar da aikin zamanantar da layin dogon da ya hada Tanzania da Zambia, da ci gaba da kokarin sabunta tashar jiragen ruwa ta Nacala dake kasar Mozambique, a kokarin karfafa tushen bangaren sufuri ga ci gaban nahiyar Afrika. To, tantance wadannan abubuwa zai sa mutum fahimtar cewa, ci gaban kasar Sin tana sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikin kasashen Afirka.

Ban da haka, shugaba Xi Jinping na kasar Sin, a cikin jawabinsa na murnar sabuwar shekara, ya ce kasarsa ta zama daya daga cikin kasashe mafi ci gaban fannin kimiyya da fasaha. To, maganarsa ta tunatar da ni game da kalmomin da Gaspard Banyankimbona, wani babban jami’in kungiyar tarayyar kasashen Afirka (AU) ya fada, wajen wani taron da ya gudana a birnin Wuhan na kasar Sin a watan Nuwamban bara, inda ya ce, sabbin fasahohin kasar Sin suna haifar da alfanu ga al’ummun kasashen Afirka, misali manhajojin biya kudi suna saukaka ayyukan hada-hadar kudi a Afirka, kana allunan samar da wutar lantarki ta hasken rana suna taimakon kokarin zamanantar da kauyukan Afirka. Hakika, dimbin shaidu sun nuna cewa, ci gaban kimiyya da fasaha a kasar Sin yana karfafa jin dadin rayuwar al’ummun kasashen Afirka.

Sa’an nan, ban da ci gaban Sin a fannonin tattalin arziki, da kimiyya da fasaha, manufofinta su ma suna amfanar da kasashen Afirka. Misali, a cikin jawabinsa na murnar sabuwar shekara, shugaba Xi Jinping na Sin ya ambaci yadda kasarsa ke kara bude kofa ga kasashen ketare, maganar da ta sa na tuna da yadda a shekarar 2025, kasar ta Sin ta sanar da shirinta na yafe wa kasashe 53 dake nahiyar Afirka, wadanda suka kulla huldar diflomasiyya da ita, harajin kwastam. Dangane da batun, shahararren masani dan Najeriya, Charles Onunaiju, ya ce, manufar da kasar Sin ta gabatar za ta daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin daukacin nahiyar Afirka, inda za a ba kasashen Afirka damar fitar da karin kayayyaki, da samun karin kudin shiga, da karfafa tasirin yankin ciniki maras shinge na nahiyar Afirka, ta hanyar ingiza bangaren samar da kayayyaki masu daraja, da dunkulewar shiyyoyin Afirka ta fuskar tattalin arziki da ciniki.

Duk a cikin jawabinsa na taya murnar sabuwar shekara, shugaba Xi Jinping ya ambaci shawarar inganta jagorancin duniya (GGI) da ya gabatar a shekarar bara, don neman kara tabbatar da adalci a duniya. Dangane da batun, na tuna da wani bayanin da wani masani mai suna Hildebrand Shayo, dan kasar Tanzania, ya rubuta, wanda a cikin makalarsa ya ce, yadda shawarar GGI ta dora muhimmanci kan daidaituwar ikon mulkin kai na mabambantan kasashe, wanda hakan zai haifar da alfanu ga kasashen Afirka, wadanda suka dade suna jin radadin matsalar rashin daidaito a tsare-tsaren duniya.

A karshen jawabinsa, shugaba Xi na kasar Sin ya karfafa gwiwar jama’a domin su kara kokarin aiki a hadin gwiwarsu, ta yadda za su samu damar cika dukkan burikan da suka sanya a gaba. To, wannan fatan alheri, a ganina, tabbas zai tabbatar da makomar huldar Sin da Afirka a sabuwar shekara ta 2026 da muke ciki. (Bello Wang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *