Sojoji Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga A Jihar Kano
[ad_1]
Sojoji sun daƙile wani harin ramuwar gayya da ‘yan bindiga suka kai wasu ƙauyuka a Ƙaramar Hukumar Shanono ta Jihar Kano.
Harin ya faru ne a daren ranar Alhamis zuwa safiyar ranar Juma’a a yankunan Yankwada da Babanduhu.
- Ci Gaban Sin Zai Haifar Da Ci Gaban Afirka
- Abubuwan Da Ke Haddasa Gobara A Lokacin Sanyi Da Hanyoyin Kare Su
Rundunar ta ce ‘yan bindigar sun shiga yankunan a kan babura inda suka dinga harbi, amma sojoji suka fattatake su.
Kakakin rundunar a Kano ya ce harin ramuwar gayya ne sakamakon kashe wasu ‘yan bindiga da sojoji suka yi a wani artabu da suka yi da su makon da ya gabata.
Ya ƙara da cewa saurin ɗaukar mataki da sojojin suka yi ya hana asarar rayuka da lalata dukiyar jama’a.
Wani shugaban al’umma a yankin ya bayyana cewar ‘yan bindigar sun zo da yawa tare da muggan makamai.
Sai dai rundunar soji ta musanta iƙirarin cewa an kashe mutane ko kuma an sace shanu a yayin harin.
Rundunar sojin ta tabbatar wa mazauna yankin cewa dakarunta na ci gaba da shirin ko ta kwana a faɗin jihar.
Ta kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai a kan lokaci.
[ad_2]
Source link