Mutum 10 sun rasu yayin da sojoji suka yi artabu da ’yan bindiga a Filato

[ad_1]



Aƙalla sojoji uku da ’yan sa-kai bakwai ne, suka rasu yayin wani artabu da ’yan bindiga a ƙauyen Wanka da ke yankin Keram a Ƙaramar Hukumar Kanam ta Jihar Filato.

Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin ranar Juma’a, lokacin da ’yan bindiga suka shiga ƙauyen suna harbe-harbe.

Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa sojoji uku da ’yan sa-kai bakwai ne sun rasa rayukansu yayin artabun.

An kuma ce wasu daga cikin ’yan bindigar sun mutu a yayin arangamar.

Wani mazaunin yankin, Gambo Musa, ya ce wasu kyaftin biyu daga rundunar sojojin na cikin waɗanda suka rasu.

Ya bayyana cewa mazauna ƙauyen sun daɗe suna rayuwa cikin barazanar ’yan bindiga, inda a cewarsa ’yan bindigar kan shiga ƙauyen su aikata abin da suke so sannan su tafi.

Musa, ya ce tun da safiyar ranar Juma’a ne jami’an tsaro ƙarƙashin jagorancin wasu kyaftin guda biyu suka shiga ƙauyen suka fafata da ’yan bindigar, inda aka kashe wasu daga cikinsu yayin da wasu suka tsere zuwa cikin daji.

Sai dai bayan wasu sa’o’i, kafin sojojin su bar yankin, ’yan bindigar sun sake haɗuwa a cikin dajin, suka dawo suka kai wa sojoji da ’yan sa-kai da ke taimaka musu hari.

“’Yan bindigar sun dawo daga cikin daji suka kai hari kan jami’an tsaro. An yi musayar wuta mai tsanani wanda ya janyo asarar rayuka a ɓangarorin biyu,” in ji Musa.

Wani mazaunin yankin, Ibrahim Ubale, ya ce harin ya yi muni, inda ya bayyana cewa ’yan bindigar sun je da muggan makamai, lamarin da ya ba su damar yin fito-na-fito da sojoji da ’yan sa-kai.

“An yi musayar wutar na wasu mintuna, amma har yanzu ba a tabbatar ko akwai wasu mazauna ƙauyen da abin ya shafa ba,” in ji shi.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar Operation Enduring Peace, Kyaftin Polycap Oteh, bai amsa kira ko saƙonnin waya ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Rahotanni sun nuna cewa ƙauyuka da dama a ƙananan hukumomin Wase da Kanam, waɗanda ke maƙwabtaka da juna, sun daɗe suna fuskantar hare-haren ’yan bindiga.

A watan da ya gabata, rundunar sojin Najeriya ta tura sojoji kusan 300 zuwa yankin domin taimakawa wajen yaƙi da ’yan bindiga, satar mutane da sauran ayyukan ta’addanci.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *