Wane Irin Tanadi Kuka Yi Wa Sallah Karama A Wannan Lokacin?
[ad_1]
Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban daban da suka shafi al”umma, cikin sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba game da abin da ya shafi Sallah Karama. Inda shafin ya ji ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu; “Wane irin tanadi aka yi wa Salllah Karama a wannan lokacin?, A kowacce shekara akan fitar da wasu nau’ikan kaya na sakawa wadanda ake fitar musu da sunaye daban-daban na yayi, shin ko wannan sallar an yi mata tanadin kaya na musamman?, Wacce shawara za a bawa matasa da kuma iyaye game da kayan Sallah, musamman wadanda Allah bai hore musu da kaya me yawa ba?”.
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Badariyya Muhammad, Jihar Kano:
Gaskiya wannan sallar an yi mata tanadi da yawa, musamman kayan adon na mata aka tanada, kamar takalmin da za a yi yayinsa me suna Shafa Wali, sai kuma Hijab me sarka me suna Capacity, sai atamfa me ‘stones’. Kayan da aka tanada kenan a wannan sallah in sha Allah. Sannan ina kira ga ‘yan’uwa mata musamman matasa ‘yan’uwanmu da su rage buri, kuma su yi hakuri da iya abin da iyaye suka yi musu, kada ki ce lallai sai ke ma an yi miki Shafa Wali ko kuma Capacity, ki yi hakuri domin duk kudi gare su ba wai sauki ne da su kamar ruwan sha ba. Abin da Allah ya horewa iyayenka ka yi hakuri da shi, kar ka je kana roko wajen saurayi ko bayar da kai dan neman kudin atamfa me ‘stones’
Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos, Jihar Filato:
Cikin yardar Allah nan da mako mai zuwa ana shirye-shiryen kammala azumi da gudanar da bikin Sallah Karama. Tun kafin ganin watan Ramadan wasu da dama sun fara shirin tunkarar bikin sallah, musamman wadanda ke fargabar samun akasi daga wajen tela. Shi ya sa mako guda da shigar azumi har wasu teloli na cewa sun rufe karbar dinkin sallah, sai na idon kunya. Saboda yadda aka yi gaggawar kai dinkuna da wuri. Kamar yadda yake bisa al’ada kowacce shekara ba a rasa irin salon dinki ko kayan da za a ce akwai yiwuwar za a yi yayinsu a bana, musamman ga yara da mata. Manya ma suna da irin nasu kayan da ake sa ran ganin su da yawa a jikin mutane, kamar dinkin yadi da babbar riga mai aikin zare na zamani. Su kuma mata dogayen riguna na Abaya da hijabai masu salon dinki daban-daban. Nasihata ga ‘yan’uwa musulmi maza da mata shi ne, kada a tsawwala wa kai, ko a yi buri fiye da abin da Allah ya hore mana. A yi dinki na mutunci, tarbiyya da tsare al’ada. Kuma a guji matsawa har a ciwo bashi don a yi irin dinkin wance ko gyaran jiki irin na wance ba. A yi shirin sallah daidai misali. Kadaran Kadahan!
Sunana Hassana Iyayi Yahaya (Maman Noor), daga Jihar Kano:
Allah ya kai mu lafiya shi ne babban tanadin, Hmmm Aikuwa wannan shekarar an fitar kala-kala ma kuwa sai fatan Allah hore abin siya. Wanda Allah bai hore ba a wanke na Bara a saka shi ne lafiya lau.
Sunana Aminu Adamu, Malam Madori, A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya al’amarin sallah a wannan shekara sai mu ce Alhamdullilah, domin hidimar sallah daidai gwargwado mun yi muna kuma kan yi har zuwa lokacin sallah. To, magana sutura ta yayi ko akwai ta ma domin ni shadda nafi amfani da ita musamman lokacin bukukuwan sallah dama bukukuwan aure ko suna, don mu shadda ce adon mu na sallah insha’Allah. To, shawarata a nan ita ce ya kamata mutum yayi amfani da irin damar da yake da ita kada yayi gasa ko koyi da wani wanda yafi karfin sa wajen gudanar da hidimar sallah, kuma mu dage da yi wa kasar mu Najeriya addu’ar samun zaman lafiya a wannan kwanaki masu albarka.
Sunana Sadiya Abubakar Maru, daga Gombe:
Ba a rasa nono a riga, wannan abu ne da kowa ya sani tun fil azal. Al’umma sun fara tanadin sallar bana tun da wuri ta hanyar sayen kayan sawa da kuma bada dinki da wuri domin gudun samun matsala daga wajen tela. Shekarar bana ma ta zo da sabon salo kamar yadda aka saba a kowace sallah. Kamar yadda yake yawo a kafafen sada zumunda, akwai hijaabi mai capacity, takalmin shafa wali, da zani mai ‘stone’ wanda mutane da dama ke nema ido rufe. Shawarata ita ce kowa ya daga hannu ya kalli yatsun hannunsa, zai ga ba daidai suke ba. Wannan yana nuni da cewa daidai ruwa daidai gari. Kada a takura kai wajen yin abin da karfin mutum bai kai ba, ayi mika daidai da abun rufa. Idan Allah ya hore miki ki yi, idan bai hore miki ba kada a duma kai.
Sunana Muhammad Isah, Zareku Miga A Jihar Jigawa:
Sallar Bana Alhamdulillahi domin ta zo cikin saukin tsadar rayuwa. Saboda kayan abinci ya zo da dan sauki. Eh a Bana mata a garin mu sun fi yin Ankon LESHI DA SHADDA SHAMPOO. Shawara da zan bawa matasa da ma iyaye shi ne su tuna idan bana Allah bai hore miki ba to, a baya ai an yi sabbin kaya kala-kala a saka hakuri idan Allah ya so nan gaba sai a dinka sabbin kaya. A samu mai kyau a saka a tafi masallacin Idi.
[ad_2]
Source link