Shettima ya tafi Guinea da Switzerland halartar taro don wakiltar Tinubu

[ad_1]



Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bikin rantsar da Shugaban Ƙasar Guinea, Mamadi Doumbouya, a birnin Conakry.

Bayan kammala bikin a Guinea, Shettima zai wuce zuwa Davos, ƙasar Switzerland, domin halartar taron shekara-shekara na 56 na Zauren Tattalin Arziƙin Duniya (World Economic Forum – WEF).

Wannan bayani ya fito ne daga Stanley Nkwocha, Babban Mataimaki na Musamman na Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwa a Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce Shettima zai wakilci Shugaba Tinubu a bikin rantsar da Shugaba Doumbouya, wanda za a gudanar ranar Asabar, 17 ga watan Janairu, a filin wasa na GLC da ke Nongo, Conakry.

Ta ce halartar Shettima a bikin na da muhimmanci wajen ƙarfafa shugabanci a yankin, haɗin gwiwar tattalin arziƙi.

Haka kuma, wannan mataki na nuna rawar da Najeriya ke takawa a ECOWAS, musamman wajen tallafa wa Guinea ta dawo da mulkin dimokiraɗiyya bayan shekara huɗu na mulkin riƙon ƙwarya.

Nkwocha ya ƙara da cewa ziyarar za ta taimaka wajen ƙarfafa kasuwanci tsakanin Najeriya da Guinea.

Ya bayyana cewa fitar da kayayyakin Najeriya zuwa Guinea, musamman kayayyakin masana’antu da na noma, ya ƙaru zuwa dala miliyan 3.29.

Daga Guinea, Shettima zai wuce birnin Davos-Klosters na ƙasar Switzerland domin halartar taron WEF na 2026, wanda zai gudana daga 19 zuwa 23 ga watan Janairu, 2026.

Taken taron na bana shi ne “A Spirit of Dialogue”, wato tasirin tattaunawa.

Taron zai haɗa shugabanni, ’yan kasuwa, ƙungiyoyin fararen hula, masana kimiyya da al’adu, domin tattauna manyan ƙalubalen da duniya ke fuskanta tare da neman mafita.

Taron zai mayar da hankali kan sabbin fasahohi kamar AI, kwamfuta da sauransu da kuma hanyoyin samar da makamashi.

Manufar ita ce duba yadda za a yi amfani da waɗannan fasahohi ta hanya mai kyau domin bunƙasa tattalin arziƙi, samar da ayyukan yi, tallafa wa kasuwanci, da tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.

A yayin taron, Shettima zai kuma gana da shugabannin duniya da masu zuba jari domin tattauna sauye-sauyen tattalin arziƙin Najeriya, damar zuba jari, da rawar da Afirka za ta taka wajen haɓaka tattalin arziƙin duniya.

Ana sa ran Mataimakin Shugaban Ƙasar zai dawo Najeriya bayan kammala dukkanin ayyukansa a Davos.

Wannan lamari na faruwa ne a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke ci gaba da jiran dawowar Shugaba Tinubu, bayan tafiyarsa hutu a ƙasashen waje.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *