Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni
[ad_1]
A yau Litinin shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci nune-nune da aka gudanar a babban gidan adana kayan tarihi na “Palace Museum”, albarkacin cika shekaru 100 da kafuwar gidan tarihin.
Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi kira da a kara babbar azama wajen kare gidan tarihin, a matsayinsa na wuri dake rike da matsayin kyakkyawar ma’adanar wayewar kai ta kasar Sin.
Kazalika, a dai yau din, kamfanin dab’i na al’ummar kasar Sin, ya wallafa wani littafi na shugaban kasar Sin Xi Jinping, mai kunshe da cikakkun bayanai, da fashin baki kan muhimman batutuwa da aka tattaunawa kan tsaron al’umma. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link