Kasar Sin Ce Kan Gaba Wajen Samun Kudin Shiga Daga Tikitin Kallon Fina-Finai A Duniya A 2026

[ad_1]

Kasar Sin ta sha gaban kasuwar fina-finai ta yankin Amurka ta Arewa da ta hada kasashen Amurka da Canada, inda ta zamo kan gaba wajen samun kudin shiga daga fina-finai a yanzu haka. A cewar dandalolin sayar da tikiti ta intanet, zuwa jiya Asabar, kudin da kasar ta samu daga sayar da tikitin kallon fina-finai ciki har da wadanda aka yi tanadi, ya zarce yuan biliyan 7, kimanin dala miliyan 970, adadin da ya dara jimillar ta Amurka da Canada da kadan, da ta kai dala miliyan 938.

Kasar ta samu wannan tagomashi ne musammam saboda hutun bikin bazara na sabuwar shekarar gargajiya ta Sinawa, wanda aka fara daga ranar 15 ga wata. Zuwa yanzu, kudin da aka samu daga sayen tikitin kallon fina-finai a lokacin hutun na Sin ya zarce yuan biliyan 4.4, wanda ya bayar da gudunmuwar sama da rabin jimillar da za a samu a bana.

Yayin hutun na kwanaki 9, an gabatar da sabbin fina-finai na bangarori da dama a karon farko, a gidajen kallo da ke fadin kasar, wanda ya samar da kyakkyawan yanayi na haduwar iyalai da nishadi a lokacin. (FMM)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *