Yadda za a hana tashin gobara a kasuwanni
Tashin munanan gobara sau biyu cikin kimanin makonni biyu a Kasuwar Singa da ke Kano ta sa masana da ’yan kasuwar neman gano ainihin dalilan da matsalar da ta yi wa kasuwar katutu da kuma ingantattun hanyoyin hana sake aukuwar haka a kasuwanni.
Kimanin shaguna dubu biyu da kayan cikinsu ne suka ƙone ƙurmus bayan tashin mummunar gobara a katafariyar kasuwar a ranar Asabar, wadda ta yi ta ci har zuwa ranar Lahadi, 15 ga watan nan na Fabrairu, 2026.
Mutum bakwai sun ɓace, ana ci gaba da neman su, kamar yadda Shugaban ’Yan Kasuwar Singa, Alhaji Junaid Zakari, ya shaida wa wakilinmu, a lokacin da muke hada wannan labarin.
Wani ɗan kasuwar, Alhaji Musa Ibrahim, ya ce ya yi asarar kayan kimanin Naira miliyan 340 a gobarar. Da yake nuna wa wakilinmu tokar kayan nasa da suka ƙone, ya ce, “Wutar ta cinye duk abin da muke da shi.”
Shi ma Alhaji Isa Abubakar, ya bayyana cewa kimar kayan da ya yi asara a gobarar ta kai na Naira miliyan 200.
Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa duk da ɗaukin da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta kai kaswuar tare da gudummawar tankokinin ruwa da kayan kashe gobara daga kamfanoni masu zaman kansu, irin su Gongoni, Umza da kuma Aspira Nigeria Ltd., wutar ta ci gaba da yin ɓarna na tsawon awanni kafin a shawo kanta.
Kafin gobarar ta ranar Asabar, a ranar Litinin, Asabar 2 ga watan nan na Fabrairu, wata gobarar ta cinye shaguna 70 a kasuwar, wadda ta shahara da harkokin kayan abinci na kamfani da kayan tireda da sauransu.
Me ke kawo gobara a kasuwa?
Wasu ’yan Kasuwar Singa sun bayyana cunkoso a matsayin babban dalilin yawan tashin gobara a kasuwar. Sun bayyana cunkuson shaguna da kiyas-kiyas da gidajen zama da aka mayar wurin ajiyar kaya masu hadarin tayar da wuta a mastayin babban dalilin gobarar.
Akwai kuma matsalar matsattsun hanyoyi da rashin ingantaccen tsarin gini kasuwar, lamarin da kawo tsaiko ga aikin agaji idan wata matsala ko buƙatar gaggawa ta taso.
Sun bayyana cewa, duk lokacin da gobara ta tashi a kasuwar, motocin kwana-kwana na shan wahala sosai kafin su isa wurin, dole suke ƙoƙarin fesa ruwa daga nesa ta yadda zai kashe wutar.
Alhaji Usman Sani Dakata, ya ce, “Yawan mutane a lokacin da harkoki suka kankama, musamman bayan tashi kasuwa, ya isa zama shaida kan irin haɗarin da muke ciki idan aka samu matsalar tashin gobara.
“Akwai buƙatar gaggawa na gwamnati ta shigo ta tabbatar da rashin cunkoso tare da fitar da manyan dakunan ajiyar kaya daga kasuwar.”
Shugabannin kasuwar sun tabbatar wa wakilinmu cewa yunƙurin Gwamnatin Jihar Kano na dauke manyan dakunan ajiyar kaya daga kasuwar a baya, wanda ya gamu da turjiya daga ’yan kasuwar, ya kawo kara ƙazancewar cunkoso da barazanar gobara a kasuwar.
A baya Gwamnatin Jihar Kano ta fara shiring sauya dauke Singa da wasu kasuwanni daga inda suke a yanzu zuwa Cibiyar Kasuwanci ta Kano da ke Ɗangwauro, da ke kan Titin Zariya zuwa Kano.
Wakilinmu ya yi kokarin tattaunawa da Kwamishinan Kasuwanci, Masana’antu da Zuba Jari na Jihar Kano, Shehu Wada Sagagi, don jin ina aka kwana kan batun, amma abin ya faskara, saboda bai ɗauki wayar ba.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa Kasuwar Kayan Marmari na ’Yanlemo da ke Na’ibawa da kuma Kasuwar Kayan Miya da ke ’Yankaba su ne wadanda layi ya zo kansu na komawa Ɗangwauro.
Wakilinmu ya kai ziyara Ɗangwauro, inda ya ga ’yan kasuwar kayan magunguna sun riga sun koma wurin, kuma ana gi gaba da buga bulo domin ci gaba da ayyukan gine-gine.
Hanyoyin hana tashin gobarar kasuwanni
Ƙwararren masani kan harkokin kare bala’o’i daga Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Dakta Sulaiman Yunus, ya bayyana cewa yawancin gobarar kasuwanni suna faruwa ne a sakamakon sakaci da sauran dalilai na halin dan Adam.
Ya danganta mafi yawan gobarar da ake samu kasuwanni da matsalar rashin ingancin wayoyin lantarki da kuma haɗa na’urar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana (sola) ba bisa ka’ida ba.
Ya jaddada muhimmancin daukar matakan kariya tun kafin gobara ta tashi, ta hanyar hada wayoyi masu inganci kuma yadda ya kamata, tare da samar da injinan kashe gobara, da kuma amfani da sabbin dabarun yaki da gobara.
A cewarsa, “Har yanzu muna amfani ne da tsohuwar dabara ta jiran sai gobara ta tashi kafin a fara kokarin kashe ta. Abin da ake bukata shi ne mu dauki matakan kariya tun kafin gobara ta tashi, ba wai mu tsaya jiran sai ta faru ba.”
Dakta Yunus, wanda kuma babban malami ne a Sashen Ilimin kasa na Jami’ar BUK, ya kara da cewa binciken digirin digirgir da ya yi, ya shafi wannan batu, kuma ya riga ya gabatar da shi ga gwamnatin jihar domin yin abin da ya dace.
Abin da muka gani —’Yan Kasuwa
Da yake bayyana munin gobarar a lokacin da take ci, wani dan Kasuwar Singa, Nasir Maharazu, ya ce, “Yanzu haka da muke magana ina ganin wutar tana ci, gini mai hawa uku gaba daya ya kama da wuta. Wannan gobarar ta ninka wadda aka yi sati biyu da suka wuce.”
“Gobarar ta fara ne daga wani shagon kayan tireda, kuma cikin ’yan mintoci ta watsu zuwa sauran shaguna, mun yi kokarin kwashe wasu kaya, amma tsananin zafin da hayakin ya yi yawa,” in ji wani ganau.
Alhaji Usman Sani Dakata, ya ce, “Yawan mutane a lokacin da harkoki suka kankama, musamman bayan tashi kasuwa, ya isa zama shaida kan irin hadarin da muke ciki idan aka samu matsalar tashin gobara.”
Me ake zargi?
Duk da cewa zuwa lokacin da muke hada ana ci gaba da bincike domin gano ainihin musabbabin gobarar, amma wasu ’yan kasuwar sun yi zargin matsalar na’urar lantarki ta sola, a yayin da masu ruwa da tsaki ke ganin yawan sanya sola a kasuwar a matsayin barazana.
Masana sun ce rashin amfani da wayoyi masu inganci da kuma batirin Lithium na sola da rashin hadawa da inganci, na iya haddasa gobara.
Rahotanni sun nuna ’yan kasuwar sukan bar sola a kunne bayan tashi daga kasuwa. Wani dan kasuwar, Nasir Ibrahim, ya ce “Muna zargin fashewar batirin lithimun ne a wani shago ya jawo gobarar da ta yadu a kusan duk shaguanan da ke Gidan Glass.”
Malam Buhari Saminu Danhajiya, ya yi zargin hada sola mara inganci. “Bayan an tashi kasuwa ’yan kasuwa ba sa kashe solarsu. Matsala ’yan kadan na iya kawo tashin wuta. Akwai bukatar gaggauta aiwatar da tsauraran matakan amfani da sola, da kuma bayar da horo na wajibi da kuma lasisi ga masu aikin hada sola,” in ji shi.
Amma, Jamiiin Hulda da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce yawancin labaran da ake yadawa kan dalilin gobarar kasuwa ba su da tushe, domin hukumar ba ta kammala bincike ba.
Ya ce asarar ta yi muni matuka, inda wasu gine-gine suka kone kurmus. “Ko da yake an samu nasarar dan dakile gobarar,” in ji shi.
Gobarar Kasuwar Singa ta jawo sakonnin jaje daga shugabanni da daidaikun mutane, a yayin da ake kira da a dauki matakan kariya da samar da kayan kashe gobara da tsare-tsare masu inganci domin shawo kan lamarin.