‘Yan Bindiga Sun Rage Kuɗin Fansar Matafiya 28 Da Suka Sace A Filato zuwa N30m
[ad_1]
‘Yan bindiga da suka sace matafiya 28 a ƙauyen Zak da ke Karamar Hukumar Wase a Jihar Filato sun rage kuɗin fansa daga Naira miliyan 42 zuwa Naira miliyan 30.
Haka kuma, sun buƙaci a saya musu sabbin babura guda uku kafin su saki mutanen.
- Jam’iyyar NNPP Ta Yi Watsi Da Dakatarwar Da Aka Yi Wa Dungurawa A Kano
- Bukukuwan Ƙarshen Shekara: ‘Yansanda Sun Haramta Buga Bangas A Kano
Mutanen da aka sace, maza da mata da kuma yara, suna kan hanyarsu ta zuwa ƙauyen Sabon Layi domin halartar Mauludi lokacin da mahara suka tare motarsu suka yi awon gaba da su.
A baya, maharan sun buƙaci Naira miliyan 1.5 kan kowane mutum, amma iyalan waɗanda aka sace sun ce ba za su iya haɗa kuɗin ba, inda suka roƙi a sake su.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Wase ya bayyana cewa an tura sojoji da jiragen sama masu saukar ungulu domin ceto waɗanda aka sace.
Haka kuma, Rundunar ‘Yansandan Jihar Filato ta ce wata tawagar jami’an tsaro ta musamman tana aiki don kamo masu laifin.
Sai dai iyalan waɗanda aka sace sun ce suna cikin fargaba da ruɗani, domin suna tsoron ko da an biya kuɗin fansar, maharan ba za su saki mutanen ba.
[ad_2]
Source link