An Fara Tafiye-Tafiye Na Bikin Bazara Na Sin A Yau
[ad_1]
An fara gudanar da babban balaguro na shekara-shekara na kasar Sin a yau Litinin domin Bikin Bazara, kwanaki 15 kafin bikin na shekara ta 2026, wanda kuma ake kira sabuwar shekara ta Sin wato sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya .
An yi hasashen za a samu jimillar tafiye-tafiyen fasinjoji da ta kai biliyan 9.5 a lokacin balaguro na wannan shekara wanda zai kare a ranar 13 ga watan Maris, adadin zai kai matakin koli a tarihi.
Daga cikin wannan jimillar, tafiye-tafiye ta hanyoyin mota za su ci gaba da kasancewa babbar hanyar balaguro, inda yawan mutanen da za su zabi hanyoyin zai kai kusan kashi 80 cikin 100.
Ana kiyasin layin dogo zai yi jigilar fasinjoji miliyan 540, yayin da sashin jiragen saman fasinja zai yi jigilar mutane da yawansa zai kai miliyan 95. Yawan mutanen da za a yi jigilarsu a wannan shekara zai kai matsayin koli a bangaren jirgin kasa da na sama, kuma adadi mai yawa da ake samu a kowace rana shi ma zai kai matakin koli. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link