ADC ba za ta taɓa lashe zaɓe a Kano ba — Gwamna Abba

[ad_1]



Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce jam’iyyar ADC ba za ta iya lashe zaɓe a jihar ba.

Ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a Fadar Gwamnati da ke Kano, bayan dawowarsa daga tarukan siyasa da aka yi a Abuja da Kaduna.

Gwamnan, ya ce yana da tabbacin zai sake lashe zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar APC, yana mai cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin inganta rayuwar jama’a.

“Falle ɗaya ne a jam’iyyar NNPP za mu yi, za kuma mu yi falle na biyu a APC. Amma ADC da suka koma, ba za ta samu ko falle ɗaya ba,” in ji shi.

Abba, ya bayyana ADC da sauran jam’iyyun adawa a matsayin marasa ƙarfi waɗanda ba za su iya samun gagarumar nasara a siyasa ba.

“Kano da Najeriya gaba ɗaya suna tare da APC… kada mutane su ruɗe da abin da ake kira ADC da sauran jam’iyyu,” in ji shi.

Ya kuma yi alƙawarin ƙara ƙoƙari idan aka sake zaɓarsa, musamman a fannoni kamar gine-gine, ilimi, lafiya, noma da samar da ruwa.

“Kun ga irin ƙoƙarinmu a cikin shekaru biyu zuwa uku da suka wuce. Idan kuka sake ba mu dama, za mu ƙara yin fiye da haka,” a cewarsa.

Gwamnan, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kan ƙoƙarinsa na inganta tattalin arziƙi da gina ababen more rayuwa.

“Shugaban ƙasa yana ƙoƙari… yana aiki domin tabbatar da ci gaba a faɗin ƙasar nan,” in ji shi.

Haka kuma, Gwamna Abba, ya ce mutanen Kano za su goyi bayan Tinubu a 2027.

“Mu a Jihar Kano muna tare da Shugaban ƙasa kuma za mu sake zaɓensa a 2027,” in ji shi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *