David Mark Ya Ƙaryata Jita-jitar Murabus, Ya Ce Ƙarya Ce Tsagwaronta
[ad_1]
Jam’iyyar ADC ta yi fatali da rahotannin da ke yawo cewa Shugabanta na ƙasa, Sanata David Mark, ya yi murabus daga muƙaminsa, tana mai bayyana zargin a matsayin ƙarya tsagwaronta da aka ƙirƙira domin jefa ruɗani da rikici a cikin jam’iyyar a wannan lokaci mai muhimmanci na siyasa.
A cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labarai na shugaban jam’iyyar ya fitar, ADC ta bayyana cewa wannan jita-jita wani “ƙagaggen labari ne maras tushe” da wasu marasa kishi ga ci gaban jam’iyyar ke yaɗawa, tana mai cewa babu wani shiri ko tunani daga David Mark ko shugabannin jam’iyyar na yin murabus daga jagoranci a halin yanzu.
- 2027: ADC Na Duba Yiwuwar Fitar Da Dan Takarar Shugaban Kasa Ta Hanyar Yarjejeniya — Kakakin Jam’iyya
- 2027: Obi Da Kwankwaso Za Su Fafata Da Atiku Wajen Neman Takarar Shugaban Kasa A ADC
Sanarwar ta jaddada cewa Sanata David Mark har yanzu shi ne cikakken shugaban jam’iyyar na ƙasa, tana mai cewa duk wanda ke yaɗa irin waɗannan rahotanni yana ƙoƙarin tayar da tarzoma da kuma raunana haɗin kan jam’iyyar, musamman a daidai lokacin da ake shirin manyan sauye-sauyen siyasa gabanin zaɓen shekarar 2027.
Haka kuma, jam’iyyar ta bayyana cewa shugabancinta na ci gaba da kasancewa a haɗe, mai ƙarfi da kuma mai himma wajen tabbatar da ingantacciyar dimokuraɗiyya da samar da sahihin jagoranci ga ‘yan Nijeriya, tana mai gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na kawo cikas ga tafiyarta zai gamu da turjiya daga mambobinta da masu goyon baya.
A ƙarshe, ADC ta buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa, tana mai tabbatar da cewa jam’iyyar na nan daram kuma za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa a fagen siyasar ƙasar, tare da aniyar tabbatar da cewa an kare tsarin jam’iyyu da dimokuraɗiyya daga duk wani yunƙuri na rushewa.
[ad_2]
Source link