NAJERIYA A YAU: Bayan Shekaru Sittin, Me Ya Sa Har Yanzu Ake Tunawa Da Su Sardauna?
[ad_1]
Ƙarin Podcasts
A tarihin kowace ƙasa, akwai wasu mutane da ba lokaci ko sauyin zamani ke iya gogewa daga ƙwaƙwalwar al’umma ba. A Najeriya, waɗannan su ne kafuwar ubanni — jagororin da suka tsaya tsayin daka wajen jagorantar gwagwarmayar neman ’yancin kai, kafa tubalan dimokuraɗiyya, da shimfiɗa tsarin ƙasa tun kafin a haifi Jamhuriyar Tarayya ta Najeriya. Gudunmawarsu ba ta tsaya kawai ga siyasa ba; sun bayar da rayuwarsu, tunaninsu domin tabbatar da cewa Najeriya ta zama ƙasa mai cikakken iko da mutunci a idon duniya.
Ko wadanne dalilai ne suka sa har yanzu ba’a manta da irin wadannan mutane a tarihin Najeriya ba?
Wannan shine batun da shirin Najeirya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link