Mun Ceto Nijeriya Yayin Da Take Gab Da Dilmiyewa – Tinubu

[ad_1]

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin duba harajin da aka ɗora wa gidan jaridu da Rediyo da talabijin domin ƙarfafa masana’antar watsa labarai da kuma inganta rawar da take takawa a kundin tsarin mulki.

Shugaban ya yi wannan alkawari ne a ranar Juma’a a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, yayin wani taron buda baki da ya yi tare da shugabannin kafafen yaɗa labarai.

  • Nijar Ta Haramta Fitar Da Dabbobi Ketare Don Takaita Karancinsu A Cikin Gida
  • Ministan Wajen Sin Ya Zanta Da Takwarorinsa Na Afghanistan Da Holland

Tinubu ya yaba wa masu gidajen jarida, editoci da ‘yan jarida bisa rawar da suke takawa wajen sanar da al’umma bayanai, halin da kasa ke ciki, samar da guraben aiki da kuma tabbatar da dimokuraɗiyya ta gaske.

A cewarsa, shugabanci na gari yana buƙatar ɗaukar matakai masu wahala a lokacin da ya dace, yana mai cewa gazawar shugabanni wajen ɗaukar mataki a lokutan da suka dace na iya zama kamar guje wa nauyin da ke kansu.

Ya bayyana cewa wasu sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar sun kasance masu wahala, amma matakai ne da suka zama dole domin daidaita tattalin arziki da kuma hana Nijeriya dilmiyewa cikin matsalar kuɗi mai tsanani.

Ya ce: “Dole ne mu ceci ƙasar nan mu dawo da ita yayin da take gab da dilmiyewa.

“A yau zan iya tsayawa, in yi alfahari a gabanku cewa, Nijeriya ta farfaɗo daga wancan mawuyacin lokacin.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *