Hukumomin Gabatar Da Kararraki Na Sin Sun Dukufa Wajen Yakar Laifukan Sayar Da Kayayyakin Jabu
[ad_1]
Wata sanarwar da hukumar koli ta gabatar da kararraki ta kasar Sin ko SPP a takaice, ta raba wa manema labarai a Asabar din nan, ta ce a shekarar 2025 da ta gabata, hukumomin gabatar da kararraki na kasar Sin, sun gurfanar da mutane 18,376 gaban kuliya, kan laifukan da suka shafi samarwa, da kuma sayar da kayayyakin jabu da marasa inganci.
Kazalika, SPP ta ce hukumomin a dukkanin fadin kasar Sin, sun ci gaba da matsa kaimin shawo kan laifukan dake barazana ga nagartar abinci, da magunguna, da nufin kare lafiyar jama’a.
SPP ta kara da cewa, a shekarar ta 2025, masu gabatar da kararraki sun gurfanar da mutane 9,595 gaban kotu kan zargin aikata laifuka 5,026 masu nasaba da abinci, da kuwa wasu mutanen 4,043 kan laifuka 2,135 masu alaka da magunguna. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link