An kama ɗan shekara 60 kan yi wa mai shekara 24 fyaɗe

[ad_1]



Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta kama wani dattijo mai shekaru 60, Ajayi Femi, bisa zargin yi wa wata budurwa mai shekaru 24 fyaɗe.

Mai magana da yawun rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Lahadi.

Ya bayyana cewa an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu ta hannun sashen da ke bincike cin zarafin mata na rundunar da ke Ikeja.

A cewar Hundeyin, lamarin ya faru ne a ranar 22 ga watan Agusta, 2025, inda ƙanwar wacce abin ya faru da ita ta kai rahoto ofishin ‘yan sanda na Meiran, daga nan kuma aka miƙa lamarin zuwa sashen bincike na musamman.

Binciken farko da ya haɗa da gwajin likitoci ya nuna cewa wanda ake zargi ya zuba wani abu a cikin abin sha na budurwar, wanda ya sanya ta suma, kafin ya aikata lalata da ita ba tare da amincewarta ba.

“Tuni aka gurfanar da shi gaban kotu inda aka ajiye shi a gidan yari har zuwa lokacin da aka sa ranar sake zama,” in ji Hundeyin.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Lagos, CP Olohundare Jimoh, ya bayyana cewa rundunar ta kuduri aniyar ganin an samu adalci ga duk wanda aka ci zarafinsa, tare da tabbatar da tsaron rayuka da mutuncin al’ummar jihar.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su riƙa kai rahoton duk wani laifi da ya shafi fyaɗe ko cin zarafi zuwa mahukunta mafi kusa domin a ɗauki mataki cikin gaggawa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *