Salla: Abba ya bai wa gidajen yari 13 kyautar shanu 14 da buhun shinkafa 82 a Kano

[ad_1]



Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da tallafin shanu da kayan abinci ga fursunoni a gidajen gyaran hali 13 na jihar, domin ba su damar gudanar da shagulgulan bikin Ƙaramar Salla cikin farin ciki.

Kayayyakin da aka raba sun haɗa da shanu 14, buhunan shinkafa 82, jarkoki 38 na man girki, da kayan miya.

Wannan mataki an ɗauke shi ne da nufin tallafa wa walwalar fursunonin tare da sanya su jin daɗin lokacin bukukuwan salla.

Hajiya Azumi Namadi Bebeji ce, ta miƙa kayan a madadin gwamnatin jihar.

Ta bayyana cewa wannan tallafi shaida ce da ke nuna cewa gwamnati na kula da dukkanin ’yan ƙasa, har ma da waɗanda ke tsare a gidajen gyaran hali.

Haka kuma, ta buƙaci fursunonin da su yi amfani da wannan lokaci na salla wajen gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya, haɗin kai, da ci gaban Jihar Kano da ma Najeriya baki ɗaya.

Ta kuma ƙarfafa musu gwiwa su kasance masu bin doka da oda tare da kyakkyawan fata na samun sauyi a rayuwarsu.

Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) reshen Jihar Kano, ya bayyana cewa shugaban hukumar na jihar, Ahmed Yusuf Lakpene, ya miƙa godiyarsa ga gwamnatin jihar bisa tallafin da kuma kulawar da take nuna wa ga rayuwar fursunoni.

Gwamnatin jihar ta sake nanata ƙudirinta na ci gaba da kula da walwalar fursunoni tare da tabbatar da adalci da jin-ƙai a gare su, musamman a lokutan bukukuwa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *