2027: INEC Ta Gabatar Wa Jam’iyyu Sabbin Ƙa’idojin Zaɓe
[ad_1]
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta gabatar wa jam’iyyun siyasa sabbin ƙa’idoji domin tunkarar babban zaɓen 2027.
Hukumar ta ce ta yi hakan ne domin jam’iyyun su ba da shawarwari da kuma taimakawa wajen inganta yadda za a gudanar da zaɓen.
- Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alƙawarin Kawo Ƙarshen Matsala Tsaro A Zamfara
- NPC Ta Yi Rajistar Haihuwa 36,000 A Kano Cikin Watanni 9
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana hakan a wani taro da shugabannin jam’iyyu a Abuja.
Ya ce sabbin ƙa’idojin sun yi daidai da dokar zaɓe ta 2026, kuma za su taimaka wajen gyara kura-kuran baya.
Wata jami’ar INEC, Zainab Aminu, ta ce an bai wa jam’iyyun takardun domin su duba su kuma su bayar da ra’ayinsu.
Sabbin ka’idojin sun shafi:
- Yadda jam’iyyu za su gudanar da zaɓen fidda gwani
- Rijista da soke rijistar jam’iyyu
- Haɗakar jam’iyyu kafin zaɓe
Ta ce jam’iyyun sun amince da yawancin ƙa’idojin, kuma idan suna da ƙorafi, za su kai ga majalisar dokoki domin gyara, domin ita ce ke yin dokoki, ba INEC ba.
Haka kuma, INEC ta ce tana ci gaba da sabunta rijistar masu zaɓe, tare da bai wa ‘yan Nijeriya masu shekara 18 damar yin rijista.
A ƙarshe, hukumar ta ce za ta bayyana lokacin da za a nuna rijistar domin jama’a su duba su kuma gyara kura-kurai kafin zaɓe.
A yanzu, harkokin siyasa sun fara zafi, inda ‘yan jam’iyya mai mulki ke goyon bayan Shugaba Bola Tinubu, yayin da ‘yan adawa ke shirin tunkarar zaɓen 2027.
[ad_2]
Source link