An sauya dokokin haraji da muka amince da su — Kwamitin Majalisar Wakilai

[ad_1]



Kwamitin Majalisar Wakilai ya tabbatar da cewa gano wasu sauye-sauye da aka yi a cikin sabbin dokokin haraji da majalisa ta amince da su wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya sanya wa hannu.

Wannan na cikin rahoton kwamitin da majalisar ta kafa domin yin bincike na musamman kan zargin cushe da aka yi a cikin sabbin dokokin haraji.

Lamarin ya samo asali ne bayan wani ɗan majalisa, Abdulsamad Dasuki, ya bayyana damuwa kan zargin yin cushe a dokokin haraji.

Kwamitin ya kwatanta hujjoji da Majalisar Wakilai ta fitar da waɗanda aka wallafa, inda ya gano sauye-sauyen da aka yi, musamman a Dokar Gudanar da Haraji ta Najeriya ta 2025.

Daga cikin sauye-sauyen da aka gano akwai rage adadin kuɗin da ake buƙatar bayyanawa da kuma tilasta masu biyan haraji su ajiye wani kaso na kuɗi da kuma bai wa hukumomin tara haraji ƙarin iko ba tare da umarnin kotu ba.

Kwamitin ya kuma bayyana cewa an cire ikon Majalisar Tarayya na sanya ido kan dokokin harajin da aka wallafa.

’Yan majalisar sun bayyana waɗannan sauye-sauyen a matsayin haramtattu kuma barazana ga dimokuraɗiyya.

Sun nemi ƙarin lokaci domin zurfafa bincike don gano yadda aka yi sauye-sauyen da kuma waɗanda ke da hannu a ciki.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *