Kasar Sin Ta Bayar Da Gudunmuwar Kayayyakin Bukata Ga Matan Sudan Ta Kudu

[ad_1]

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Sudan ta Kudu, ya bayar da gudunmuwar kayayyakin amfani ga mata da ‘yan mata masu rauni a Juba, babban birnin kasar, a wani mataki na jaddada kudurin Sin na taimakawa wajen ganin ci gaban harkokin mata a kasar.

Gudunmuwar da aka bayar da hadin gwiwar asusun kula da jama’a na MDD (UNFPA) da ma’aikatar kula da jinsi da yara da walwalar al’umma ta Sudan ta Kudu, na da nufin inganta rayuwa da kare mutuncin mata da ‘yan mata masu rauni.

Jakadan Sin a Sudan ta Kudu Ma Qiang, ya ce gudunmuwar na kunshe da kayayyakin bukatun yau da kullum da na tsaftar jiki, ciki har da audugar mata da sabulu da toci irin na sola, kuma za a raba su karkashin shirin asusun UNFPA.

Ya kara da cewa, suna da muhimmanci ga rayuwa da kare hakkokin mata, yana mai cewa, tabbatar da walwalar mata hakki ne da ya rataya a wuyan kasa da kasa. (FMM)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *