Gwamna Abba ya fice daga jam’iyyar NNPP

[ad_1]



Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya fice daga jam’iyyar NNPP, biyo bayan lokaci da aka shafe ana jita-jitar sauya sheƙarsa zuwa jami’yyar APC.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce gwamnan ya miƙa takardar murabus ɗinsa ga shugaban jam’iyyar NNPP na mazaɓar Diso-Chiranchi a Ƙaramar Hukumar Gwale, wanda za ta fara aiki daga ranar 25 ga watan Janairu, 2026.

“Ina rubutawa ne cike da godiya domin sanar da shugabancin jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a hukumance kan shawarar da na yanke na ficewa daga jam’iyyar,” in ji gwamnan.

Gwamna Yusuf ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi da kuma goyon bayan da ya samu tun shekarar 2022.

“Ina matuƙar godiya da damar da jam’iyyar, shugabancinta da mambobinta a fadin Jihar Kano suka ba ni,” in ji shi.

Sai dai gwamnan ya ce rikicin shugabanci da shari’o’in kotu da ke gudana sun raunana jam’iyyar.

“A ‘yan kwanannan, jam’iyyar na fuskantar ƙalubale masu yawa sakamakon sabanin shugabanci da shari’o’in da ke gaban kotuna,” ya bayyana.

Ya kara da cewa rikicin ya raba kan mambobin jam’iyyar tare da haifar da rashin tabbas a matakin jiha da kasa baki ɗaya.

“Ƙarin jin an ware mambobi ya haddasa babbar rarrabuwar kai a cikin tsarin jam’iyyar,” in ji Yusuf.

Gwamnan ya ce ya dauki matakin ne bayan dogon tunani, domin amfanin al’ummar Jihar Kano.

“Na yanke wannan shawara ne bayan yin tunani sosai, kuma domin amfanin mutanen Jihar Kano,” ya kara da cewa.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa mambobi 21 na Majalisar Dokokin Jihar Kano, mambobi takwas na Majalisar Wakilai, da shugabannin kananan hukumomi 44 sun fice daga NNPP tare da gwamnan.

Sakataren NNPP na mazabar Diso-Chiranchi, Kabiru Zubairu, wanda ya tabbatar da karbar takardar murabus din gwamnan, ya yaba da ayyukan da Yusuf ya yi.

“Ina goyon bayan ra’ayin Mai Girma Gwamna kan rikicin da ke damun jam’iyyarmu,” in ji Zubairu, yana mai cewa jam’iyyar ba ta da wani zabi illa ta amince da murabus din “daya daga cikin gwamnonin NNPP mafi kwarewa.”

Ya yaba wa gwamnan bisa nasarorin da ya samu a fannonin gine-gine, kiwon lafiya, ilimi da karfafa tattalin arziki.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *