Gwamnan Kano Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP
[ad_1]
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya fice daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), inda ya ce rikicin cikin gida ne ya sa shi ficewa daga jam’iyyar.
Wannan na ɗauke ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya hannu a ranar Juma’a.
- Kasar Sin Ta Bayar Da Gudunmuwar Kayayyakin Bukata Ga Matan Sudan Ta Kudu
- Kafa Kamfanin Sarrafa Gwal A Legas: Ƙungiyar Dattawan Arewa Ta Ƙalubalanci Tinubu
Sanarwar ta ce gwamnan ya miƙa takardar murabus ɗinsa ga shugaban NNPP na mazaɓar Diso-Chiranchi a ƙaramar hukumar Gwale, wadda za ta fara aiki daga ranar 25 ga watan Janairu, 2026.
Gwamna Abba ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi da kuma goyon bayan da ya samu tun daga shekarar 2022.
Sai dai ya ce rikicin shugabanci da shari’o’i a kotu, sun raunana jam’iyyar tare da raba kan mambobinta.
Ya ce ya ɗauki matakin ne bayan dogon tunani, inda ya ce zai ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Jihar Kano.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa mambobi 21 na Majalisar Dokokin Jihar Kano, mambobi takwas na Majalisar Wakilai, da shugabannin ƙananan hukumomi 44 sun fice daga NNPP tare da gwamnan.
Sakataren NNPP na mazaɓar Diso-Chiranchi, Kabiru Zubairu, ya tabbatar da karɓar takardar murabus ɗin gwamnan.
Ya yaba wa gwamnan bisa nasarorin da ya samu a ɓangarorin gine-gine, kiwon lafiya, ilimi da bunƙasa tattalin arziki.
[ad_2]
Source link