Boko Haram sun kai sabbin hare-hare a wasu yankunan Borno da Yobe
[ad_1]
An zargi mayaƙan Boko Haram da ISWAP da kai hare-hare wasu yankuna biyar da ke Jihohin Borno da Yobe.
Sun kai hare-haren ne garuruwan Mafa, Dikwa, Marte, da Ajiri a Jihar Borno, da kuma Katarko a Jihar Yobe.
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan ta’addan sun fara kai hari wani shingen sojoji da ke Mafa, sannan suka sace makamai da sabbin babura da sojoji ke amfani da su.
Wata majiyar tsaro ta ce: “Sun zo da yawa kuma ɗauke da muggan makamai. Sun sace makamai da baburanmu. Yawansu dana gani abun mamaki ne.”
Ba a tabbatar da adadin sojojin da suka rasu ba, amma wani jami’in tsaro ya tabbatar da cewa sun kashe ’yan ta’adda da yawa a yayin artabun.
Wani mazaunin yankin, ya ce babu wanda aka kashe daga cikin mutanen gari, amma ’yan ta’addan sun sace kayan abinci da sauran kayayyaki, sannan suka ƙone wasu motoci.
“Lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 11 na daren ranar Laraba. ’Yan ta’addan sun fara kai hari shingen sojoji inda matafiya ke jiran a buɗe musu hanya domin su ci gaba da tafiyarsu,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa mayaƙan sun kai harin a motoci huɗu ɗauke da bindigogi da kuma babura sa.a da 100, ɗauke da makamai.
Sun kuma kai makamantan waɗannan hare-haren a Marte, Dikwa, Ajiri duk a Jihar Borno, da kuma Katarko a Jihar Yobe.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link