An Samu Iska Mafi Kyawu A Beijing Yayin Da Mai Munin Gurbacewa Ta Gushe
[ad_1]
A shekarar 2025, an samu mafi kyawun iskar shaka a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin tun daga lokacin da aka fara sa ido a kan haka, inda aka samu mafi kankantar matsakaicin ma’aunin kananan kwayoyin gurbacewar iska na diyamita 2.5, watau PM2.5 a takaice, a bisa mizanin shekara-shekara, da kuma samun iska mafi kyawu a kwanaki mafiya yawa da aka taba samu, kamar yadda mahukuntan kula da muhalli na cikin gida suka bayyana.
A cewar rahoton muhalli da rayuwar halittu na Beijing na shekarar 2025 da aka fitar a yau Alhamis, matsakaicin ma’unin gurbacewar iskar na PM2.5 na shekara a birnin, ya ragu zuwa ma’aunin karamingiram 27 a kowane ma’aunin kubik mita daya, wanda ke nuna raguwar kashi 11.5 cikin 100 a mizanin shekara-shekara.
Har ila yau, an more iskar shaka mafi kyawu a birnin har na tsawon kwanaki 311, wanda ya kai kashi 85.2 cikin dari na adadin kwanakin shekara. Sannan, a rana guda daya ce kacal aka gamu da mummunar gurbacewar iska, wadda ita ce mafi kankanta da aka taba samu, inda hakan ke nuna cewa kusan an yi bankwana da kwanaki masu mummunar gurbacewar iska. Wannan ci gaba yana nuna gagarumin sauyi da aka samu idan aka kwatanta da shekarar 2013, lokacin da birnin Beijing ya yi fama da kwanaki 58 na mummunar gurbacewar iska, sai kuma kwanaki 176 kacal da aka samu mafi kyawun iskar shaka a cikinsu. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link