Shirin sakin ’yan bindigar Katsina ya tayar da ƙura

[ad_1]



Shirin sakin ’yan bindigar daji da ake zargi da satar dabbobi, yin garkuwa da jama’a domin karɓar kuɗin fansa tare da kisan ba gaira ba dalili, ya jawo ce-ceku-ce a faɗin Jihar Katsina.

Gwamnatin jihar ta sanar cewa za ta sako wasu mutane kusan 70 da ke tsare a hannun hukuma, wasu ana yi masu shari’a, wasu kuma suna jiran a gurfanar da su kan zargin ayyukan ta’addanci.

Wannan mataki ya haifar da muhawara mai zafi, inda jama’a ke bayyana ra’ayoyinsu kan dacewar shirin.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta ɗauki wannan mataki ne domin cika wani ɓangare na yarjejeniyar sulhu da aka ƙulla da ’yan bindigar a lokacin tattaunawa da al’ummomin yankunan da ake kai wa hare-hare.

Sai dai Gwamna Dikko Raɗɗa ya jaddada cewa ba shi da hannu a cikin yarjejeniyar sulhun, domin a cewarsa babu sulhu da ’yan bindiga sai dai idan su da kansu suka nemi hakan tare da miƙa makamansu a matsayin alamar tuba.

Ra’ayoyin Jama’a

Bayan sanar da shirin, jama’a daga yankunan da matsalar tsaro ta fi ƙamari suka fito suna bayyana albarkacin bakinsu.

A ƙaramar hukumar Batsari aka fara zaman sulhu da jagoran ’yan bindigar yankin, Abu Raɗɗa, ƙarƙashin shirin da sojoji suka shirya, Alhaji Hassan Dogon Faci, ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a Batsari, ya ce: “Kamar yadda yarjejeniyar ta tanada, ’yan bindigar sun daina kawo mana hari, kuma sun sako duk wanda suke tsare da shi. A nasu ɓangaren kuma sun nemi a sako wasu daga cikin mutanensu da ke tsare.

“A yanzu dai babu wanda suke riƙe da shi a yankinmu, sun cika alƙawari. Saboda haka ina ganin babu laifi a cika nasu alƙawarin da aka ɗauka.”

Sai dai wasu na ganin matakin bai yi musu daɗi ba, musamman waɗanda aka kashe musu ’yan uwa, aka karɓe wa kuɗi ko aka kwashe musu dukiya. Malam Hassan ya ce:

“Wannan lamari ne da babu yadda za a yi. Mu dai mun bar wa Allah hukunci, domin Shi ne mafi alheri. Amma fa’idar sulhun ta bayyana, yanzu an samu ci gaba da hulɗa kamar da.”

Mayar da hannun agogo baya ne

Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana shakku kan barin ’yan bindigar da makamansu. “An ce wai suna da abokan faɗa a tsakaninsu, amma duk da haka ana jin labarin suna kai hare-hare a wasu wurare da makaman. Idan haka ne, mene ne dalilin kai hare-haren bayan sulhu? Ni dai ina ganin wannan sulhu ba ta rinu ba.”

A Ƙaramar Hukumar Jibiya, an yi irin wannan yarjejeniya da jagoran ’yan bindigar yankin, Lanƙai. Amma hakan bai hana wasu ’yan ta’adda irin su Abu Wuta da abokansa (wanda daga baya suka mutu a fada tsakaninsu) ci gaba da kai harehare ba. Misali, makonni biyu da suka gabata, an kai hari a garin Ƙusa inda aka kwashe dabbobi, sai dai daga baya aka ƙwato su.

A Malumfashi kuwa, matsalar saɓa yarjejeniya ta sake bayyana. Abdul Aziz, wani ɗan yankin, ya ce a wata hira da DW Hausa, “Waɗannan ba sulhu suka yi da gwamnati ba, ɓarayi ne kawai masu kisan al’umma da karɓar kuɗin fansa. Shin bayan jama’ar gari da aka zalunta, da jami’an tsaro da suka rasa rayukansu, yaya za a yi da su?”

Wani mazaunin Malumfashi ya ƙara da cewa, “Ko wata guda ba a yi da wannan sulhu ba, suka ci gaba da kawo mana hari har cikin gari.”

’Yan bindiga sun kai sabon hari

Aminiya ta ruwaito cewa, a yayin da ake kan wannan batu, ’yan bindiga sun kashe mutane uku tare da sace wata amarya da mahalarta ɗaurin aure 16 a wasu kai sababbin hare-hare a yankin Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara.

’Yan bindiga sun kai hari kan taron ɗaurin a ƙauyen Unguwar Nagunda inda suka kashe aƙalla mutane biyu tare da sace wasu 17, ciki har da amaryar. Daga bisani mutum 8 daga cikin waɗanda aka sace sun tsere.

Kazalika sun kashe wani mutum a ƙauyen Jaga da ke kan babbar hanyar Ƙanƙara– Sheme aƙaramar hukumar.

Da yake tabbatar da lamarin, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Nasir Muazu, ya ce gwamnatin jihar ta kafa kwamitin tantance sunayen ’yan bindigar a duk ƙananan hukumomin jihar domin gabatarwa ga kotuna.

“Waɗannan kwamitoci suna tattara sunayen, kuma har yanzu aikin bai kammala ba, balle a san adadinsu. Bayan kammala tattarawa, sunayen za a miƙa wa gwamnatin jiha, wadda ita kuma za ta gabatar da su ga kotunan da ke kula da shari’o’in domin duba su.

“Kotuna za su binciki shari’o’in don tabbatar da cewa babu abin da ya sabawa doka kafin aiwatar da shirin,” in ji shi.

Wani mazaunin yankin Jaga ya ce, “Ko da yake muna jin daɗin zaman lafiya mai rauni, amma ’yan bindiga sun fara dawowa.”

Ya ƙara da cewa, al’ummar yankin ana zargin maharan na daga cikin ’yan bindiga masu adawa da yarjejeniyar zaman lafiya da aka ƙulla a ƙauyen Kakumi na ƙaramar hukumar Bakori, inda ƙananan hukumomi biyar suka shiga — Ƙankara, Malumfashi, Kafur, Funtua da Bakori mai masaukin baƙi.

Sharuɗɗan da gindaya

Kwamishinan ya ce lokacin da al’ummomi suka cimma yarjejeniyar zaman lafiya da ’yan bindiga, ɓangarorin biyu sun amince da wasu sharuɗɗa tsakaninsu.

Ya ce sharuddan su ne ba wa ’yan bindiga damar shiga kasuwanni domin saye da sayarwa, ba su damar ziyartar asibitoci don samun magani da kuma ganin ’yan uwansu, da kuma ba su ’yancin motsi ba tare da tsangwama ko tsoratarwa ba da kuma ba su damar mu’amala da jama’a cikin ’yanci.

Sauran su ne dakatar da hare-hare kan garuruwa da kauyuka, Dakatar da garkuwa da mutane, sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma sakin ’yan bindiga da gwamnati ke tsere da su.

Mu’azu ya bayyana cewa ana aiwatar da sharuɗɗan ne a hankali, kuma yanzu an kai matakin sakin ’yan bindiga da ke hannun gwamnati.

Dalilin shirin sulhu

Babban Daraktan Kafofin Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Maiwada Ɗanmalam, ya ƙara yin bayani kan shirin da gwamnati ta ɗauka na sakin wasu daga cikin ’yan ta’addan da ke tsare a hannun hukuma.

A cewarsa, “Maganar tsaro magana ce mai buƙatar sirri, ba ta dace da dandalin yanar gizo ko tattaunawa a bainar jama’a ba. A duk duniya, ba kowa ke sanin cikakken abin da ke faruwa ba.

“Sau da yawa mutane suna ganin kamar gwamnati ta yi shiru, amma hakan na cikin dabarun tsaro. Har ma gwamnatoci kan iya yin ƙarya don tabbatar da zaman lafiya. Misali, idan gwamnati ba ta da kuɗin sayen harsashi, za ta iya sanar da jama’a cewa ta sayi harsashi na biliyoyin naira domin tsoratar da abokan gaba.”

Ya bayyana cewa kowa ya san yadda ƙananan hukumomi daban-daban suka shiga yarjejeniyar sulhu da ’yan ta’adda domin samun zaman lafiya. Duk da cewa gwamnatin Katsina ta ɗauki matsayar cewa ba za ta nemi sulhu da kowanne ɗan ta’adda ba, ta bar ƙofar buɗe ga duk wanda ya ajiye makami ya rungumi zaman lafiya.

A cewarsa, gwamnati ta saurari buƙatun al’ummar ƙananan hukumomi da suka nemi damar yin sulhu da ’yan ta’addan da suka nuna sha’awar hakan. Gwamnati ta ba su goyon baya tare da tabbatar da cewa duk matakin da aka ɗauka bai saɓa wa doka ba.

A nasa ɓangaren, kwamishinen ya ce gwamnati ta shiga cikin tsarin ne “sakamakon zaman lafiya da kwanciyar hankali da aka samu a faɗin jihar saboda yarjejeniyar sulhun.”

“Gwamnatin Jihar Katsina gwamnati ce ta jama’a, don haka duk abin da jama’a suka yi wajen neman zaman lafiya, ba za ta hana su ba ko ta tauye ƙoƙarinsu. A matsayinta na gwamnati, duk abin da jama’a suka yi muddin bai saɓa wa doka ba, za mu tallafa musu domin ci-gaban al’umma.”

Nasarorin sulhun

Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnati ta ga amfanin yarjejeniyar, inda wasu al’ummomi suka shafe kusan shekara guda ba tare da fuskantar hare-haren ’yan bindiga ba.

Misali, ƙaramar hukumar Jibia tun bayan yarjejeniyar da aka cimma ranar 28 ga Fabrairu, 2025, ba ta fuskanci wani hari ba. Haka ma ƙananan hukumomin Safana da Batsari. A cewarsa, a kusan ƙananan hukumomi 19 da a baya suka sha fama da hare-hare, matsalar ta ragu da kusan kashi 95 cikin 100.

“Wannan ƙoƙari da al’ummomi suka yi bai kamata gwamnati ta ɓata shi ta hanyar gaza cika alƙawuran da aka yi wa ’yan bindiga ba,” in ji Kwamishinan.

Alhaji Maiwada ya ce, “Sulhun ya ba da damar dawo da zaman lafiya a wurare da dama. Kasuwanni da aka rufe saboda tsaro sun koma aiki, gonaki da aka bar zuwa yanzu ana noma, harkokin yau da kullum sun dawo yadda ya kamata.”

Ya ce, lokacin sulhun, ɓangarorin biyu sun gabatar da buƙatu. Al’umma sun nemi ’yan ta’addan su sako duk wanda suke tsare da shi, yayin da ’yan ta’addan suka nemi gwamnati ta sako wasu daga cikin mutanensu da ke tsare suna jiran shari’a. Shugabannin al’umma sun bayyana cewa ba su da ikon yin hakan, amma za su kai koken ga gwamnati.

Gwamnati ta tuntuɓi masana tsaro na cikin gida da na waje, kuma ta samu tabbacin cewa irin wannan mataki ana ɗauka a wasu wurare domin tabbatar da zaman lafiya.

A cewarsa, bayan bincike, gwamnati ta gano cewa akwai fiye da mutum dubu a hannun ƙungiyoyin ’yan ta’adda a wurare daban-daban. Daga nan ta amince za ta sa baki wajen sakin mutum 42 daga cikin ’yan ta’addan da ke tsare, amma sai bayan sun fara sakin mutanen da suke riƙe da su.

A cewar Alhaji Maiwada, an samu nasarar kuɓutar da mutane da dama ƙarƙashin wannan yarjejeniya, kamar haka: Safana – 36; Kurfi – 42; Faskari – 136; Sabuwa – 310; Ɗanmusa – 60; Malumfashi 36; Bakori – 125; Musawa – 28; Matazu – 33; Dutsinma – 62; Jibiya – 31; da sauran su.

Dalilin sakin ’yan ta’adda

Gwamnati tare da shugabannin al’umma sun zauna, suka auna ribar cika alkawarin da aka ɗauka. An cimma matsaya cewa ribar kuɓutar da ɗaruruwan mutane ta fi rashin ribar da za a samu idan ba a cika alƙawarin ba.

Misali, a ƙaramar hukumar Malumfashi, tsohon ɗan ta’adda Mustapha Babaro ya jagoranci kuɓutar da mutane 36, ciki har da maza, mata da yara. A kan haka ya roƙi gwamnati ta sakar masa mutum biyu kacal daga cikin waɗanda ke tsare.

Maiwada ya ce, “To ina aibun wannan matakin ko shirin? Idan aka auna fa’idar da aka samu, za a ga cewa ribar ta fi rashin ribar.”

Batun ajiye makamai

Kwamishinan ce batun ajiye makamai nan take bai shiga cikin sharuɗɗan farko na yarjejeniyar sulhu ba.

“Jihar Katsina na da yawan Fulani makiyaya masu dabbobi da yawa da ke zaune kusa da dazuka. Idan aka bar su ba tare da makamai ba, mutane daga wasu jihohi ko ma ƙasashen waje za su iya zuwa su sace musu dabbobi.”

Sai dai ya bayyana cewa gwamnatin jiha na shirin toshe hanyoyin da ’yan bindiga ke samun makamai kafin ta tattara waɗanda ke hannunsu a halin yanzu.

Ra’ayoyin masana

Shirin sakin ’yan bindigar da ke tsare ya haifar da ka-cena-ce daga ɓangarori dabandaban. Wani mai nazarin harkokin tsaro, Abubakar Ibrahim, ya ce sakin su bai kamata a ɗauke shi a matsayin musayar fursunoni ba.

“Wadannan mutane masu laifi ne kuma ya kamata a yi mu’amala da su a haka. Da dama daga cikin waɗanda ake shirin sakowa sanannu ne, kuma akwai yiwuwar su koma daji,” in ji shi.

Dokta Kabir Adamu, wani ƙwararre a fannin tsaro, ya ce, “Wannan mataki zai ƙarfafa masu guiwa. Dole ne a samar da doka ta musamman kafin a aiwatar da irin wannan shiri.”

Dokta Kabir Adamu, ya bayyana cewa akasarin waɗanda ake magana a kansu ba manyan ɓarayin daji ba ne, ƙananan yaransu ne da aka kama. Domin a duk lokacin da aka kai hari, ana jin labarin cewa manyan shugabannin sun gudu ba a same su ba.

Dakta Bashir Kurfi mai sharhi kan harkokin tsaro kuma ɗan asalin Jihar Katsina ya bayyana fargaban cewa akwai yiwuwar jihohi maƙwabta su tasirantu da wannan shirin saboda ’yan ta’addan za su iya shiga su yi ɓarna sannan su dawo Katsina sun ɓoye kuma babu wanda zai tuhumar su ganin cewa an yi sulhu.

Kurfi ya ƙara da cewa gwamnatin ba ta ɗauki matakan da ya kamata ba don ganin ɗorewar wannan zaman lafiya ba, saboda a cewarsa, ba a shigo da ƙwararrun a fannin tsaro da zaman lafiya ba wajen wannan yarjejeniya.

Tsohon Mataimakin Darakta a Hukumar Tsaro ta DSS, Mamman Mannir Murtala, ya bayyana matakin a matsayin wata hanya ta zahiri da ka iya zama mafita ga kawo ƙarshen tashin hankali. Ya roƙi masu suka da su bar masu jagorantar shirin zaman lafiya su mai da hankali wajen tabbatar da ɗorewar zaman lafiya a jihar.

Shugaban Kwamitin Tsaro na Ƙaramar Hukumar Ɗanmusa, Buhari Salisu Yantumaki, wanda kuma shi ne sakataren ƙananan hukumomi 19 da suka fi fama da hare-haren ’yan bindiga, ya ce shirin ba zai haifar da barazana ba, kuma yana da matuƙar muhimmanci wajen ɗorewar yarjejeniyar sulhu.

Ya ce, “Masu adawa da yarjejeniyar yawanci mazauna birane ne. Ku je ƙauyukan da abin ya shafa ku ga sakamakon idan ba a yi hankali ba. Mutanen karkara sun gaji, sun shiga mawuyacin hali; tashin hankali ya kai su ga ƙarshe.”

Gwamnatin Jihar Katsina ta dage cewa matakin ba sassauci ba ne, illa hanya ta samar da zaman lafiya mai ɗorawa da guje wa cigaba da asarar rayuka da dukiyoyin mutane.

Daga Ahmed Kabir S/Kuka (Katsina) da Abubakar Abdulhaman Adoro da Sagir Kano Saleh (Abuja)


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *