Shugaban Afirka Ta Tsakiya Ya Taya Sinawa Murnar Sabuwar Shekarar Doki
[ad_1]
A kwanan baya ne shugaban jamhuriyar kasar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera ya taya al’ummar kasar Sin murnar sabuwar shekarar doki ta gargajiyar kasar, tare da isar da fatan alherinsa ta kafar bidiyo daga birnin Bangui, fadar mulkin kasar.
Cikin sakonsa, shugaba Touadera ya yi tsokaci cewa, a gabannin zuwan bikin bazara na sabuwar shekarar doki ta gargajiyar kasar Sin, ya isar da fatan alheri ga al’ummar Sinawa ‘yan uwan al’ummun kasashen Afirka a madadin gwamnati da jama’ar Afirka ta Tsakiya da kuma shi kansa. Inda ya bayyana fatansa cewa, kasar Sin za ta kara samun wadata, al’ummar Sinawa za su kara jin dadin rayuwa. Ya kuma kara da cewa, dabbar doki tana alamta karfi da kokari da kuma dosa gaban wurin da ta nufa, shi ya sa yana sa ran kasar Sin za ta samun sabon sakamako a sabuwar shekarar gargajiyar kasar dake tafe.
Kana shugaba Touadera ya jaddada cewa, ya kasance zumuncin gargajiya da huldar hadin gwiwa mai karfi cikin dogon lokaci dake tsakanin kasar Sin da Afirka ta Tsakiya. Don haka Afirka ta Tsakiya tana son ci gaba da zurfafa hadin gwiwa da cudanya dake tsakaninta da kasar Sin a fannoni daban daban bisa tushe na yanzu mai inganci, ta yadda za a ingiza bunkasar dangantakar abota tsakanin sassan biyu bisa manyan tsare-tsare. (Mai fassara: Jamila)
[ad_2]
Source link